Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Saboda haka bambanci wannan ma’anoni guda biyu a bayyane yake, wato a ma’ana ta farko siffa ce ta abubuwa guda biyu, amma a ma’ana ta biyu kuwa siffa ce ta abu guda (wato daidaita wani abu ba tare da an hada shi da waninsa ba kamar yadda muka gani). Saboda haka yanzu mun fahimci ma’anonin wadannan kalmomi guda biyu: wato "Sawwaitahu da musharrafan".

Saboda haka muna iya fahimtar cewa wannan hadisi yana magana ne dangane da yadda wannan kabari yake domin kuwa yana magana ne a kan abu guda, ba wai kabari ba da kasa (wato ba a daidaita shi da kasa ba wato a daidaita shi kansa kabarin) Domin da haka ake nufi sai a ce "sawwaitahu bil ard". Saboda haka abin da Imam yake nufi a cikin wannan hadisi shi ne, duk inda ya ga wani kabari yana da tudu da kwari kamar tozon rakumi ya dai-daita shi ya gyara shi ya zama kamar dakali. Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana yadda za a yi kabarin musulmi ta yadda za a baje samansa ba a yi masa tulluwa ba kamar bayan rakumi ko kifi.

 Domin kuwa wannan zamani a kan yi kaburbura ne da tudu kamar yadda bayan rakumi yake, don haka ne Imam ya ba Abu hayyaj umarni da ya daidaita duk kabarin da ya gani a haka. Saboda haka wannan hadisi wace alaka yake da shi wajen rusa shi kansa kabari ko ginin da aka a samansa?!

 Kuma cikin su maruwaitan wannan hadisi da masu sharhinsa sun bayyana ma’anar wannan hadisi kamar yadda muka yi bayani a sama.

 1-Muslim ya ruwaito wannan hadisi karkashin babin "Amr bi taswiyatul kubur" wato ruwayoyin da suke magana a kan daidaita saman kabari, saboda haka muna iya cewa shi ma muslim abin da ya fahimta da ma’anar wannan hadisi kenan (wato kasantuwar kaburbura kamar yadda dakali yake ba kamar yadda bayan rakumi yake ba).

 2-Muslim a farkon wannan babi ya ruwaito cewa: Fudhala tare da wasu mutane sun kasance a Rom, Sai wani daga cikin mutanensa ya rasu sai ya rufe shi ya yi kabarinsa kamar yadda ake dakali (Rectangle) sai ya ce haka na ji daga Manzo (S.A.W). ya ce: Ku yi kaburbura kamar haka wato samansu a baje ba tare da tudu ba.

 Saboda haka dukkan wadannan hadisai suna bayyanar mana da ma’anar Kalmar Musharrafan da ta zo a cikin hadisi, ba tana nufin kasancewar kabari ya yi bisa ba daga kasa ko kada ya yi, tana nufin shi kansa kabarin kada ya kasance yana da tudu kamar bayan rakumi.

3-Nabawi kan sharhin wannan hadisi yana cewa: Bai kamata ba kabari ya yi bisa da kasa ba ko kuma ya zamana ya yi tudu kamar bayan rakumi. Ya cigaba da cewa dole ne bisansa ya kasance kamar kamun hannu guda sannan samansa ya zamana a baje ba mai tudu ba. [43]

 4-Kurdabi a cikin tafsirinsa ya ruwaito wannan hadisi da aka ambata yana cewa: Wannan hadisi abin yake nunawa shi ne baje kabari shi ne Sunna, sannan yi masa tulluwa bidi’a ne.[44]

 5-Ibn Hajar askalani bayan ya yi bayani a kan mustahabbancin baje saman kabari yan rubuta cewa: Hadisin Abi Hayyaj ba yana nufin cewa ba a baje ya zama daidai da kasa, abin da yake nufi shi ne a baje saman kabari ta yadda za a daidaita shi babu wani tudu a samansa, duk da yake cewa ya dan yi sama da kasa.[45]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next