Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



Idan muka dauki wannan ma’ana dogaron Ibn Taimiyya yana iya zama dai-dai. Amma tare da lura da yadda tarihin musulmai ya tafi a kan mustahabbacin tafiya zuwa kabarin Manzo (S.A.W), domin ziyara tana nuna mana rashin ingancin wannan hadisi.

 Na farko kamar yadda muka gani a cikin hadisin da ya gabata, ana iya tsammanin wata ma’ana daban, sakamakon wannan ma’ana kuwa ba za a samu wani fito na fito ba a hadisai da ayoyi da kuma tarihin musulmi da suke nuni a kan halascin ziyarar Manzo. Kuma tare da daukar ma’anar farko musamman kasantuwar mu dauki cewa kalmar da zamu iya kaddarawa ita ce masallaci, domin kasantuwar dacewarta da abin da ya zo a cikin jumlar, kuma shi ne abin da ya fi dacewa ya kuma fi karfi. Saboda haka wannan hukunci wanda Ibn Taimiyya ya dauka zai zama sam ba shi da ma’ana a nan.

 Haka nan idan muka dauki ma’ana ta biyu wato muka dauka cewa ai a nan ana nufin "wuri" wato bai halitta ba mutum ya tafi wani wuri sai wadannan wurare guda uku, wannann kuwa zai bayar da ma’anar da ba ta dace ba, sannan fitowar wannan kalma daga mai hikima musamman Manzo ba zai yiwu ba. Wato ya zama an hana zuwa kowane wuri sai wadannan wurare guda uku (Masallacin ka’aba, Kudus da Masallacin Manzo). alhalin musulunci ya halatta wasu tafiye-tafiye da dama a cikin musulunci wasu daga cikinsu ma mustahabbi ne. Misali kamar tafiya domin neman ilimi, ko tafiya domin kasuwanci ko tafiya don sada zumunci, tafiya don yawon bude ido, tafiya domin jihadi da dai sauran tafiye-tafiye da suke halas wadansu ma mustahabbi a musulunci.

 Saboda haka a nan dole ne mu dauki ma’ana ta farko wato masallaci, cewa kada mutum ya yi tafiya domin ya je wani masallaci sai masallatai guda uku, domin kuwa su ne su kafi sauran masallatai matsayi. Da wannan ne zamu fitar da batun tafiya domin ziyarar Manzo domin ba ita ake magana ba a cikin wannan hadisi.

 Bayan dangane da ingancin wannan hadisi koda an dauki ma’ana ta farko, akwai shakku a cikinsa. Domin kuwa yana nufin wannan magana ta fito daga bakin Manzo inda take nuni da cewa tafiya zuwa kowane masallaci ba ta inganta sai masallatai guda uku. Alhali kuwa ruwayoyi sun zo a kan cewa Manzo (S.A.W). Wasu ranakun Asabar yakan tafi kasa, wata sa’a bisa abin hawa domin ya je masallacin "Kubaý" domin ya yi salla raka’a biyu a wajen. Wannan masallaci a zamanin da Manzo yake a raye yana da tazarar kilo mita 12 tsakaninsa da Madina.[7]

 

Ziyarar Masallatai Guda Bakwai

 A sassa daban-daban na garin Madina akwai wasu masallatai guda bakwai wadanda mahajjata sukan ziyarta yayin da suka je Madina, Idan ma muka kara da (masallacin Raddi shams, da na Bilal da na Ijaba) Yawansu zai wuce bakwai.

 Mahajjata suka yi salla raka’a biyu a wadannan masallatai musamman sukan fi ba da muhimmanci a kan masallacin Imam Ali (A.S) Yanzu tambaya zata iya zuwa cewa: Idan har yin salla a wadannan masallatai ba shi da wani fifiko a kan sauran masallatai, to me ya sa mahajjata suke zuwa ziyarar wadannan masallatai sannan su yi salla a cikinsu? alhali kuwa wannan bai zo ba a cikin shari’a, saboda haka wannan zai zama "Bidi’a" kenan a cikin addini.

 Amsar wannan tambaya kuwa a fili take:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next