Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Bisa dogaro da wadannan dalilai muna iya fahimtar cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya ta cikin Suratun Nur shi ne gidajen annabawa da waliyyan Allah, sakamakon tasbihi da tsarkake Allah da ake yi a cikinsu yake da wani matsayi na musamman, kuma Allah ya yi izini da yin kokari wajen a daukaka su.

 5-Sannan dalili wanda yake a fili a kan cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya su ne, ayoyi guda biyu da suka zo kamar haka:

Allah madaukaki yana yi wa Annnabi Ibrahim da matarsa magana kamar haka:

A-"Rahmar Allah da albarkarsa ta tabbata a gare ku ya ku ma’abota gida[17];

B-Allah Kawai ya yi nufi ya tafiyar muku da kazanta yaku Ahlul Bait, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa[18]; Kai ka ce wadannan gidaje su ne cibiyar hasken ubangiji.

 Tare da kula da wadannan dalilai guda biyar da muka kawo muna iya cewa: Masati da daukakar wadannan gidaje sakamakon wadanda suke zaune a cikinsu ne, suna tasbihin ubangiji suna tsarkake shi. A hakikanin gaskiya wannan aya tana magana ne dangane da gidaje irin gidajen Annabi Ibrahim da Manzo (S.A.W). Wannan kuwa sakamakon tasbihi da tsarkake ubangiji da ake yi a cikinsu. Shi ne ya sanya Allah madaukaki ya daga martaba da darajarsu.

 Mai yiwuwa a ce: Karkashin wannan aya ana cewa: "Yana tasbihinsa a cikinsu safiya da yamma": wato abin da ake nufi da "Buyut" Masallatai, domin kuwa musulmin farkon zuwan musulunci sun kasance suna halarta sallar jam’i baki dayansu. saboda haka tasbihi da tsarkake ubangiji ana yin sa ne a cikin masallaci.

 Amma wannan fahimta ba daidai ba ce, domin kuwa ana aiwatar da sallar wajibi ne kawai a cikin masallatai, sannan mustahabbi ne a gabatar da sauran sallolin mustahabbi a cikin gidaje. Sannan ya kamata ma mutum ya kasa ibadarsa zuwa gida biyu, wato wani bangare na farilla ya aiwatar da su a cikin masallaci, sannan bangaren nafiloli ya gabatar da su a cikin gida.

Mai yiwuwa wasu suga wannan bai inganta ba, amma hakikanin al’amarin haka yake domin kuwa ruwayoyi da dama sun karfafa hakan. Muslim a cikin sahih dinsa, ya kawo babi mai zaman kansa wanda yake nuna mustahabbancin sallar nafila a cikin gida. A kan haka ya ruwaito ruwayoyi da dama, amma a nan kawai zamu kawo wasu a matsayin misali:

 Manzo mai tsira da aminci yana cewa: "Fiyayyar sallar mutum a cikin gidansa, sai dai sallolin wajibi"[19].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next