Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



1-"Kalmar: Kabran musharrafan"

2-"Illa sawwaitahu"

Wadannan kalmomin sune suka zo a cikin wannan hadisi;

 Dangane kalma ta farko zamu yi bayani ne a kan kalamar "musharraf" wadda take da ma’anar daukaka wato abu madaukaki. Don haka ne wadanda suke daga babban gida kamar iyalan Manzo ake kiransu da sharifai, Sannan tozon rakumi saboda kasantuwarsa yana da daukaka a kan sauran jikinsa ana kiransa da "Sharaf".

 Ya zo a cikin Tajul Arus cewa: Sharaf ma’anarsa shi ne wani wuri mai tudu, wato madaukaki. Sannan ana kiran tozon rakumi da sharaf, Sannan wurare masu bisa kamar gidajen sarakuna ana kiransu da Sharaf, Haka nan akan kira tudun da yake a kan bangaye da wannan kalma.[40] Saboda haka wannan kalma tana nufin abu mai daukaka ko kuwa kawai tana nufin tozon rakumi ko bayan kifi?.

 Tare da kula da ma’anar kalmar "Sawwaitahu" kamar yadda zamu yi bayanin a kanta zamu fahimci cewa wannan kalma ta Sharaf a cikin wannan hadisi tana nufin ma’ana ne ta musamman.

 Dangane da kalma ta biyu kuwa muna iya bayani kamar haka: Kalma ta Sawwaitahu da ta zo da ma’anar aiki wato baje wani abu ko dai-daita shi, ana mafani da ita a cikin harshen larabci da ma’anoni guda biyu.

1-Daidaita wani abu da wani abu daban ta hanyar tsawo ko girma ko makamancin haka.

Saboda haka idan da wannan ma’ana kalmar sawwa ta zo tana da aikau guda biyu (maf’ul) wanda a cikin harshen larabci wannan maf’ul na biyu yana bukatar harafin jarra wanda zai dai-daita wannan abin da waninsa.[41]

2-Ma’ana ta biyu kuwa shi ne baje wani abu ta yadda zai daidaita babu tudu da kwari, saboda haka a nan wannan fi’ili na sawwa yana bukatar maf’uli guda daya, ba shi bukatar na biyu. Saboda haka duk lokacin kafinta ya daidaita wani katako, kawai zai ce na goge katako, (wato sawwaitul khashab). [42]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next