Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Wannan ruwaya tana nuna mana cewa Manzo (S.A.W) da sauran sahabbansa suna yin sallolinsu na nafila a cikin gidajensu, sakamakon haka ne gidajen annabawa da na salihan bayi suka zama wurin zikirin Allah da tsarkake shi. Sannan kuma dalilin wannan ne Allah ya ba da izini a kan daukaka su.

 A yanzu dole ne mu ga me ake nufi daga matsayin wadannan gidaje! me ake nufi da daukaka wadannan gidaje?

A baya mun yi bayanin cewa, kafa hujja da wannan aya yana bayyanar da abubuwa guda biyu ne. Abu na farko kuwa shi ne, bayyanar da ma’anar "buyut" wanda muka yi cikakken bayaninsa a baya, yanzu lokaci ya yi da zamu yi bayani a kan abu na biyu wanda shi ne daukaka wadannan gidaje da Allah yake horo da shi.

 Hakika kalmar "Rafa’a" cikin Kur’ani tana zuwa ne da ma’anar daga gini kamar yadda ta zo a cikin wannan ayar: "Shin halittar su ita ce tafi wahala ko kuwa sama wadda ya gina ta?! Sannan ya daga rufinta ya kuma daidaita ta?![20]

Amma kalmar "rafa’a" a cikin wannan aya ba yana nufi yin gini ba, domin kuwa an dauka cewa akwai gida ne, Kur’ani yana magana a kan siffofin wannan gida ne. saboda haka abin da ake nufi da wannan kalma a cikin wannan aya shi ne daga matsayinsu da girmama su, mafi yawan masu tafisiri sun dauki wannan ma’ana duk da cewa wasu daga ciki sun tafi a kan ma’anar da muka ambata a baya. [21]

A bayyane zamu iya cewa: Wuraren da Allah yake ambatar "Buyut" yana nufin gidajen da bayin Allah suke kwana suna yin tasbihin ubangiji kuma suna tsarkake shi. Saboda haka daukaka wadannan gidaje ba ya nufin daga gininsu ko rufinsu ba ne, abin da ake nufi shi ne daga matsayi da martabarsu. Daya daga cikin wannan girmamawa da daga matsayinsu kuwa shi ne ya zamana an tsarkake su daga dukkan wata kazanta, sannan duk inda suka dan lalace a gyara su.

Dukkan wannan aiki za a yi shi ne saboda girmama wadanda suka kasance a cikin wadannan gidaje suna tasbihin ubangiji suna salloli kuma ba su kin fitar da zakka, domin girmama wadannan mutane ne Allah ya yi horo da a girmama wadannan gidaje, sannan a kare su daga rushewa.

 Kowa ya san cewa an rufe Manzo (S.A.W) a cikin gidansa, wato a wurin da ya kasance yana ambaton Allah da yabonsa. Saboda haka tare da bin hukuncin wannan aya gidan Manzo ya cancanci girmamawa da daukaka matsayinsa, sannan a kiyaye shi daga kowane irin rushewa da lalacewa. Sannan kuma a kaurace wa sanya masa duk wani nau’i na kazanta, kai da yawa daga bangarorin Madina kaburburan manyan bayin Allah ne.

Kamar yadda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi sayyida Fadima (A.S) ita an rufe ta ne a cikin gidanta[22]

 Haka nan Imam Hadi da Imam Askari (A.S) an rufe su a gidajensu wadanda suka kasance suna ibada da zikirin ubangiji a cikinsu. saboda haka wadannan gidaje bisa la’akari da wannan aya sun cancanci a daukaka su, sannan dole ne a kauce wa rusa su domin ya saba wa wannan aya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next