Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)



 Kamar yadda yake a tarihi shi ne musulman da suke rayuwa a sauran sassan duniya wato ba wadanda suke rayuwa ba a garin Madina sukan daure kayansu domin tafiya zuwa ziyarar kabarin Manzo mai girma a nan ga wasu misalai a kan hakan:

 Bilal wanda yake mai kiran salla ne na Manzo kuma Manzo ya kasance yana kaunarsa. Bayan tafiyar Manzo ya zabi ya tafi wani wuri yiwa musulunci hidima, sakamakon haka ne ya yi hijara daga garin Madina. Wani dare sai ya ga Manzo a cikin mafarki yana ce masa: Wannan wane irin rashin kulawa ne Bilal? Yanzu lokaci bai yi ba da zaka ziyarce ne?

 Lokacin da Bilal ya tashi daga barci yana cikin bakin cikin da ya mamaye masa zuciya, sai kawai ya tanaji abubuwan bukata domin yin tafiya kuma ya tafi zuwa Madina. Lokacin da Bilal ya shiga a cikin Raudar Manzo yana kuka da murya mai karfi a wannan hali ya dinga goga fusakarsa a kan kabarin Manzo (S.A.W). A nan haka sai kwatsam abin kaunarý Manzo wato Hasan da Husain (A.S) sai suka yi wajensa sai ya kama su ya runguma, sai suka ce masa, Muna tsananin son mu ji muryar kiran sallarka, kiran sallar da kake yi wa kakanmu manzon Allah (S.A.W).

 A lokacin sallar Asubahi sai Bilal ya hau wurin da ya kasance yana kiran salla a zamanin Manzo (S.A.W) ya kira salla. A lokacin da kiran sallarsa ya mamaye Madina Ya girgiza garin Madina a wannan lokaci, a lokacin da ya yi kalmar shahada a cikin kiran sallarsa sai duk mutane suka daga murya suna kuka, a lokacin da kuwa ya yi shahada a kan manzancin Manzo (Ashhahadu anna Muhammadar Rasulullah) ai sai duk mutanen Madina suka yi waje suna kuka.

Kamar yadda ake rubutawa: Bayan ranar da Manzo ya yi wafati madina ba ta taba ganin irin kukan da ta gani ba a wannan lokaci.[2]

 2-Umar bn Abdul Aziz ya kasance yana hayar mutane domin su zo daga Sham zuwa madina domin su yi masa sallama ga Manzo.

 Subki a cikin Futuhus Sham yana rubuta cewa: Lokacin Umar bn Abdul Aziz ya yi Sulhu da mutanen Kudus sai Ka’abul Akhbar ya shigo wajen kuma ya musulunta, a wannan lokaci Umar ya ji dadi kwarai da musuluntarsa. Sai Umar ya ce masa: Kana iya bi na mu tafi madina mu ziyarci kabarin Manzo ta yadda zamu fa’idantu da ziyararsa? Sai Ka’ab ya amsa wa khalifa abin da ya nema daga gareshi, ya yi shirin tafiya tare da khalifa. A lokacin da Umar ya shiga garin madina, farkon abin da ya fara yi shi ne ya shiga masallacin Manzo ne domin ya yi wa Manzo sallama.[3]

 Duk da yake ba mu da bukatar mu kafa sheda a nan da irin wadannan misalai, domin kuwa al’ummar musulmi duk tsawon karnoniý sha hudu sun dauki wannan al’amari na ziyara Manzo a matsayin mustahabbi kuma suna tafiya Madina domin su aiwatar da wannan mustahabbi.

 Subki dangane da tafiyar ayari-ayari zuwa ziyarar Manzo ya yi maganganu da dama a kan hakan, ya kara da cewa masu ziyara bayan sun gama aikin hajji sukan kama hanyar Madina ne domin su kai wa Manzo ziyara, ya kara da cewa: wata sa’a sakamakon fahimtar ladar da yake cikin yin hakan sukan dauki hanyar da tafi nisa zuwa Madina, domin su samu lada mai yawa a kan haka. Sannan ya cigaba da cewa, wadanda suke tunanin cewa dalilin da ya sa mutane suke tafiya madina shi ne domin su ziyarci masallacin Manzo kuma su yi salla a ciki wannan kuskure ne, domin kuwa abin masu ziyarar suke fada ya saba wa wannan tunanin. Domin manufarsu a kan wannan ziyara shi ne su ziyarci kabari Manzo, sannan wannan shi ne gurinsu na ziyarar Madina.

 Domin kuwa idan manufarsu a kan wannan tafiya shi ne ziyartar masallaci, me ya sa ba su tafiya Kudus domin su ziyarci masallacin baitil mukaddas wanda yin salla a cikinsa bai gaza wa yin salla a masallacin Manzo ba?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 next