Boyayyar TaskaBayan halakar da mutanen da Dufana da kuma wafatin Annabi Nuhu (A.S) sai Ashararai daga zuriyarsa Hamu da Yafusu da sahabbansa suka yi galaba a kan Wasiyyinsa Samu (A.S) da Shi’arsa suka kafirce wa Allah da Manzonsa Nuhu (A.S), suka kuma dawo da bautar gumaka da sunansu na da Ya’uka, da Yagus, da Nasra, da Suwa’a, da Wudda. Sarauta ta ci gaba a hannun zuriyar Kabila da I’waja har zuwa kan Kan’ana baban Namarzu kafirin sarkin nan a lokacin Annabi Ibrahim (A.S) wanda ya kasance daga zuriyar Hamu Dan Nuhu ne. Amma Samu Dan Nuhu (A.S) ya ci gaba da rike sakon Allah, kuma sakon bai gushe ba daga wasiyyi zuwa wasiyyi mai bi masa har zuwa kan Nakhur kakan Annabi Ibrahim (A.S) zuwa Tarikha babansa, har zuwa kansa (A.S). Bayan Annabi Ibrahim Da Musa (A.S) Amma idan ka ji abin da ya faru bayan wafatin Annabi Ibrahim (A.S) sai ka zubar da hawaye, domin annabawa da salihai daga zuriyar Ibrahim (A.S) ba su samu damar yin hukunci ba sai na dan lokaci kankani, ashararan ‘ya’yan Ishaka (A.S) suka samu galaba a kan annabawa da salihai suka karkashe su, suka kuma kora wasunsu zuwa dazuka da tsaunuka haka nan a bin ya ci gaba har zuwan Annabi Musa (A.S). Duba Tarihin Isu Dan Annabi Ishak da galabar da ya samu Labarin wahalhalun da Annabi Musa (A.S) ya sha a hannun Bani Isra’ila ba boyayye ba ne ga wannan al’umma da aka saukar wa Kur’ani mai girma, shi ma ya kasance yana da Wasiyyai biyu da dayansu shi ne Annabi Haruna (A.S) wanda ya rasu a lokacin rayuwar Annabi Musa (A.S) wanda ya tafi ya bar shi da al’umma cikin kwana arba’in kawai, amma a cikin wadannan kwanaki sai aka yi wa wasiyyin tawaye aka ma dauki Musa Samiri wanda yake munafiki ne a al’ummar Annabi Musa (A.S) kuma Annabi Musa (A.S) ya kore shi daga rundunarsa, amma ya dawo ya yi sihiri ya kuma iya jawo hankulan ‘Ya’yan Isra’ila suka bar Annabi Haruna (A.S) suka bi Musa Samiri, a nan muna iya tambayarka mai karatu? yaya kake gani idan da ya zamanto Musa ya rasu ne fa? kuma yaya al’amarin zai kasance da ba zai dawo ba. To haka nan kuwa abin ya faru, sai ga shi kafin rasuwarsa ya shelanta wa al’ummarsa wasiyyinsa Yusha’u Dan Nun (A.S) amma bayansa sai al’ummar ta ki bin Wasiyyin ta hada kai da munafukai aka wahalar da shi aka kuma yi masa tawaye. Yahudawa ba su bi Yusha’u Dan Nun (A.S) ba sai ‘yan kadan shi ma a lokacin suna cikin dimuwa ta shekara arba’in ne da Allah ya saukar musu saboda kin biyayya ga Annabin Allah Musa (A.S). A wannan shekarun dimuwar ne Allah ya dauki ran Annabawansa; Annabi Musa (A.S) da wasiyyinsa na farko Annabi Haruna (A.S) zuwa gare shi, amma bayan shekara arba’in dimuwa ta kau sai Annabi Yusha’u (A.S) ya Da haka ne fajirai da munafukai suka yi galaba a Wasiyyan Dawuda Da Sulaiman (A.S) Amma bayan wafatin Annabi Sulaiman (A.S) Tarihi ya fadi yadda Sahabbansa da ashararan danginsa suka yi wa wasiyyinsa Asifu Dan Barhaya (A.S) da jama’arsa, suka kawar da shi daga rike shugabancin da Annabi Sulaiman ya bar shi a kai. Da tun farko sun san cewa Annabi Sulaiman ya rasu da ba su Bayan Masihu Mai Albarka Isa Dan Maryam Amma bayan Isa (A.S) ya daukaka zuwa ubangijinsa sai ga ukuba mafi tsanani daga al’ummarsa da Rumawa a
|