Boyayyar Taska



Matansa: An rawaito cewa ya auri mata bakwai, Ta farko ita ce: Ummu Abdullahi ‘yar Al-Husaini (A.S) amma sauran duk Kuyangi ne.

‘Ya’yansa: 1-Imam Bakir (A.S) 2-Abdullahi 3-Al-Hasan 4-Al-Husaini 5-Zaid 6-Umar 7-Al-Husainil Asgar 8-Abdurrahman 9-Sulaiman 10-Ali 11-Muhammad Asgar 12-Khadija 13-Fadima 14-Aliyya 15-Ummu Kulsum.

Tambarin zobensa: Wama taufiki illa bil-Lahi.

Littattafansa; Sahifatus sajjadiyya da Risalatul hukuk.

Tsawon rayuwarsa: shekara 57.

Tsawon Imamancinsa: Shekara 35.

Sarakunan zamaninsa:  Mu’awiya da Yazidu dan Mu’awiya, da Mu’awiya dan Yazidu dan Abi Sufyan, da Marwana dan Hakam, da Abdulmalik dan Marwana, da Walida dan Abdulmalik.

Tarihin shahadarsa: An yi sabani a kan hakan amma an ce 12 Muharram ko 18 ko 25 ga Muharram, haka nan shekara an ce 94 ko 95 H.

Inda ya yi shahada: Madina.

Dalilin shahadarsa; Guba da aka ba shi a lokacin halifancin Walid dan Abdulmalik.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next