Boyayyar TaskaTambarin zobensa: Masha’Allah la Kuwwata illa bil-Lahi. Tsawon rayuwarsa: shekara 55. Tsawon Imamancinsa: Shekara 20. Sarakunan zamaninsa: Abu Ja’afar Al-mansur da Muhammad Al-Mahadi da Musa Al-Hadi da Harunar-Rashid da Al-amin da Al-ma’amun dukkaninsu sarakunan Abbasiyawa ne. Tarihin shahadarsa: karshen Safar 203H. Inda ya yi shahada: Garin Duss a Khurasan. Sababin shahadarsa: Shan guba a lokacin halifa Al-ma’amun. Inda aka binne shi: A Al’karyar San’abad a Duss Khurasan. A yau wurin yana cikin birnin Mash’had. Muhammad Dan Ali Al-Jawad (A.S) Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Ali da Musa dan Ja’afar (A.S). Babarsa: Kuyanga ce sunanta: Sukaina Al-marsiyya, an ce sunanta Al-khaziran. Alkunyarsa: Abu Ja’afar Assani da Abu Ali.
|