Boyayyar TaskaTarihin haihuwarsa: 3 Sha’aban 4 H, ko 5 Sha’aban. Inda aka haife shi: Madina. Yakokinsa: Ya yi tarayya da babansa a yakin Jamal da Siffaini da Naharawan kuma shi ne jagoran Askarawan Rundunar Alkawari da imani masu tsanani a kan kafirai da mabiya bata a al’amarin kisan kare dangi da aka yi wa Ahlul Baiti (A.S) a Karbala. Matansa: 1-Shazinan ‘yar kisra 2-Laila ‘yar Murra Assakafiyya 3-Ummu Ja’afar Al-kada’iyya 4-Arribab ‘yar Imri’ul Kais Al-kalbiyya 5-Ummu Ishak ‘yar Dalha Attaimiyya. ‘Ya’yansa: 1-Ali Akbar 2-Ali Asgar 3-Ja’afar 4-Abdullahi Addari’i 5-Sakina 6-Fadima. Tambarin zobensa: Likulli ajalin kitab. Tsawon rayuwarsa: shekara 57. Tsawon Imamancinsa: shekara 11. Sarakunan zamaninsa: Mu’awiya da Dansa Yazid. Tarihin shahadarsa: 10 Muharram 61H.
|