Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Idan muka lura da wadannan mas’aloli, cikin sauki za mu iya fahimtar manhajar Imamai na Ahlulbaiti kuma wasiyyan Annabin rahama (s.a.w.a). Wannan manhajar tana da sassa biyu malizimta juna: na farkon yana dangantaka  da akida, na biyun kuma yana da alaka da samar da karfin zartarwa da zamantakewa. A sashen farko, Imaman suna fuskantarda kokarinsu da himomminsu ne wajen yada manufofin sako da kafa su, da tono duk wani kaucewa gaskiya da karkata wadanda masu bin son rai suke sabbabawa; da bayyana ra’ayin musulunci kan sababbin mas’aloli da raya alamomi wadanda suka rushe, sakamakon karo da amfanin ma’abota iko da masu fada a ji; da faiyace abin da ya boyu wa hankula na daga littafin Allah mai girma da sunnar Ma’aiki. Ana iya takaita zance kan nauyin sashen farko da cewa kare rayayyen sakon musulunci ne mai ginuwa, tsawon zamani.

A sashen na biyu kuwa gwargwadon abin da yanayin siyasa da zamantakewar al’ummar musulunci suke hukuntawa, suna kokarin samar da shimfida da ake bukata wajen karbar ragamar shugabancin al’umma da kansu a kusa, ko kuma shimfida domin imamin da zai ci  gaba da tafiyar tasu a nan gaba ya kuma karbi shugabanci bayan zango mai tsawo.

Wannan a takaice shi ne manufar rayuwar tsarkakan Imamai, kuma wadannan su ne tsarin manufofinsu a game, saboda su suka rayu kuma dominsu suka yi shahada. Idan tarihin rayuwar Imamai wanda ya zo mana ba ya tabbatar da ra’ayin da muka tafi a kai, to akidarmu kan Imamai ta isa ta sauwara mana rayuwarsu ta wannan fuskar kadai. Mene ne zatonka idan tarihi yana ba da shaida da take gamsar da ko wane mai bincike cewa rayuwar Imaman Ahlulbaiti tana kan wannan mafuskantar?.

ZANGO-ZANGO NA TAFIYAR IMAMANCI.

Tafiyar Imamanci ta fara ranar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya bar duniya cikin watan Safar, shekara ta goma sha daya bayan hijira har zuwa wafatin Imam Hassan Askari (a.s) a watan Rabi’ul Awwal, shekara ta dari biyu da sittin bayan hijira. Cikin wadannan shekaru, tafiyar Imamaci ta ci zango hudu, wanda a kowanne Imamai sun dauki matsayi fitacce gaba ga mahukuntan al’ummar musulmi.

ZANGO NA FARKO:-

Wannan ya kunshi matakin kame baki ko mu ce matakin taimakawa mahukunta. A wannan zango jinjirar al’ummar musulunci ta yi fama da hadarin magabta wanda ya yi mata kawanya. Yayin da wadannan magabta suka ji barazanar da sakon musulunci  yake masu, sai suka dana tarkon su daga wajen daular musulunci suna dakon wata dama domin su aukawa wannan sabuwar al’umma. A wani janibin kuwa akwai adadi mai yawa na sabon-shiga musulunci wadanda hankalinsu ba zai iya daukar halin rarraba cikin al’ummar musulunci ba, saboda haka duk wata tsagar da ka iya faruwa za ta zama barazana ga tushen al’ummar da ma samuwarta. Na uku, karkatar da ta sami al’umma ba ta yi tsananin da har mutum kamar Amirul Muminina Aliyu ibn Abi Talib(a.s) wanda ya fi kowa kaunar kubutar sakon musulunci da al’ummarsa, ba zai iya jure mata ba. La’alla wanna halin da ya sami jama’ar musulmi shi ne abin da Manzon tsira Muhammadu (s.a.w.a) ya yi ishara da shi lokacin da ya yi wasici ga wannan dalibinsa wanda yake farda, da ya yi juriya  idan ya auku.

Wannan zangon ya dauki tsawon rayuwar Imam Ali (a.s) fara daga wafatin Manzon Allah ( s.a.w.a) har zuwa karbarsa halifanci. Imam ya yi sharhin matsayin da ya dauka cikin takardar da ya rubuta wa mutanen kasar Masar yayin da ya nada masu Malik Ashtar hakimi. Ya ce:- “Sai na kame hannuna yayin da na ga masu juyawa sun juyawa musulunci baya, suna kira

 zuwa shafe addinin Muhamamdu (s.a.w.a). Sai na ji tsoron idan ban taimaka wa musulunci da ahlinsa ba, zan ga tsagewa da rugujewa tattare da shi. Da haka zai faru, to da musibar da za ta sami musulunci ta fi tsanani a gare ni bisa ga kubucewar shugabancin ku.……sai na bayar da gudumowata a abubuwan da suka  faru”(1)

Yayin da shugabanci ya kauce masa sai ya hakura domin musulunci, lokacin da al’umma ta fuskanci hadura masu girma sai ya mike domin kare musulunci da al’ummarsa, yana mai shiryarwa da aiki a fagagen siyasa da soji  da zamantakewa. Cikin Nahjul Balaga da sirar Imam Ali, akwai bayanai masu tabbatar da irin nau’in kokarinsa a zamanin shugabancinsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next