Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Akwai wadansu hujjoji daban masu bayyana abin da kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) da shi’arsu kan imamanci ya kunsa. Jayayya tsakaninsu da abokan hamayyarsu na siyasa (Umayyawa da Abbasiyawa) ta bijiro da shi. Wani lokaci ana wannan jayayya ne ta hanyar kafa hujja a fagen addini da ilmul kalam a wasu lokatan kuma tana daukar salon adabi mai zurfi ta hanyar wake. Duk jayayyar ana yin ta ne kan tabbatar da cancantar imamanci a siyasance da shugabanci ga imaman Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmaya  da masu kankamewa kan karagar hukumar musulmi bisa zalunci da kwace.  Saboda yin zamani daya da harakar Abbasiyawa da samun nasararta, lokacin Imam Sadik (a.s) ya kasance a cike yake da irin wannan jayayya da mujadala.

Mawakan Abbasiyawa suna kokarin tabbatar da cancantar shugabanci ga Abbasiyawa suna dogaro da hujjojinda, bisa al’ada, masu kwadayin mulki da kuma masu kankamo da karagar sarauta suke gabatarwa. Mawakan shi’a kuwa sukan  fuskance su suna gugar wadancan hujjojin suna masu kafa hujja kan fandarar da mulkin Abbasiyawa ya yi daga mandikin musulunci ( dalilan da ya dogara a kansu ) wanda yana kafe ne bisa yarfar da zalunci da aikata laifi da ha’intar hakkokin al’ummar musulunci.

 Mukabala ta hanyar wake tsakanin Abbasiyawa da Alawiyyawa  tana da muhimmanci a nan saboda irin muhimmiyar rawar da wake ke takawa a wancan lokacin wajen bayyana abin da rai ya kunsa da tunane-tunane saboda kuma irin tsarin da yake da shi kan mabiya cikin talakawa.  Ma’abocin littafin “Abbasiyawan Farko” yana ambatar rawar da adabi ya taka a karnin farko da na biyu. Ya ce:-

“Adabi ya kasance yana tasiri a zukata yana kokarin samun goyon bayan jama’a da karkatarsu ga wannan kungiya ko waccar, mawaka da masu jawabi matsayinsu irin wanda jaridu suke da shi ne a yau . Ko wannensu yana bayyana wani ra’ayin siyasa ne yana kuma kare wata kungiya ayyananna, yana bijiro da dalilin ingancikin kirar da yake yi daya bayan daya yana rushe ra’ayoyin abokan hamayya da magana maiu tasiri da salo mai fasaha”[36]

Mawakan fadar Abbasiyawa sun kasance suna kokarin tabbatar da cancantar Abbasiyawa ga halifanci da hujjar alakarsu da Annabi ta hanyar ‘ya’yan baffa, sun kafa hujja kan hakan da cewa gado ba ya riskar ‘ya’yan diya tare da samuwar baffanu. Saboda haka halifanci a bayan Annabi hakkin Abbas, baffan Annabi ne, a bayansa kuma, na ‘ya’yansa ne, watau yayan Abbas. Marwan ibn Abi Hafsa ya ce:-

Kaka zai yiwu, ai bai yiwuwa,

Gadon baffanu a hannun dan diya.

 Abban ibn Abdilhamid  Lahiki ya ce:-

Ya’yan Abbas su ke da gado nai,

Baffa ga dan baffa ai hijjabi ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next