Jagorancin Imam Sadik (a.s)Da farko ya zama wajibi mu ambata cewa mukamin halifanci a musulunci yana da wadansu sifofin da suke sanya shugaba ya banbanta da shugabanni a wadansu tsare-tsaren shugabanci na daban. Shi halifanci ba wai tsarin siyasa ne kadai ba a’a, shi tsari ne na siyasa da addini a gwame. Baiwa shugaban musulunci lakabin halifa yana karkafa wannan batu: shi halifan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a duk wani aikin da Manzo yake aiwatarwa ga jama’a wa lau nauyin da ya shafi addini ne ko kuwa na jagorancin siyasa. Shi halifa a musulunci yanan dauke da mas’u’liyyar siyasa da ta addini gaba daya. Wannan tabbataccen al’amari ya sa halifofin da suka zo bayan na farko, wadanda rabonsu a cikin ilmomi addini ya yi karanci ainun, ko kuwa basu da wani rabo sam, ya sanya su rufe wannan nakasu ta hanyar malaman addini masu aikata musu abin da suke so. Sai suka baiwa fukaha’u da malaman tafsiri da na hadisi aiki a fada saboda tsarinsu na shugabanci ya Wata fa’idar samuwar masu wa’azin sarki a tsarin shugabanci, ita ce: azzalumin shugaba mai Mawallafa da marubuta tarihi daga magabata sun Wannan shi ne musabbabin rabuwar ilmomin musulunci: na fkihy da hadisi da tafsiri, tun zamunan na farko, zuwa ra’ayoyi biyu. Ra’ayin Farko:- Ra’ayin da ke da alaka da tsarin azzulumar hukuma mai kwace. Ra’ayin na Biyu:- Ra’ayi dan asali amintacce wanda ba ya ganin akwai wata maslaha mai daraja da daukaka da ta wuce bayyana ingantattun hukunce-hukuncen Ubangiji. Wannan ra’ayi ya kasance, ko an ki ko an so, yana cin karo da tsarin da yake shugabanci da kuma masu wa’azin fada, a duk wani taku da ya yi. Saboda haka tun farkon al’amari ya dauki mafuskanta irin ta talakawa tare da taka tsan- tsan da kiyayewa. Fahimtar wannan zai sa mu gane da kyau cewa sabawan Fikihun Ja’afar da fukaha’un sarauta a zamanin Imam Sadik ba wai sabawa ce ta tunani da akida kadai ba, a’a ta hada har da abin da ya kunsa na hari irin wanda abokin hamayya yake yi. Mafi muhimmanci daga kusurwowin wannan abin da ya kunsa shi ne tabbatar da cewa tsarin da ke shugabanci fanko ne kawai wanda ya rasa dukkan ma’anonin addini, ga kuma gajiyawarsa wajen gudanar da al’amuran tunani ga al’umma. Ko kuma mu ce rashin cancantarsa hawa mukamin “halifanciâ€. Wata kusurwa ita ce ayyana wuraren da aka baude cikin fikihun sarauta, wadannan baude-baude da aka gina Ba mu da wani tabbataceen isnadi mai bayyana lurar tsarin Umayyawa da wannan janibin hamayya, wanda Imam Sadik (a.s) ya aiwatar a fagen ilmi da fikihu. Sai dai abin da aka fi tsammani shi ne tsarin Abbasiyawa mai mulki-----musamman lokacin Mansur wanda yake mai wayo da gogewa da fahimtar halayyar duniya, abubuwan da ya koya a lokacin dambarwar siyasa mai tsawo sakaninsa da mulkin Umayyawa kafin shi kansa ya sami mulkin--wannan tsarin nasu yana kiyaye mas’alolin masu wuyar fahimta da ke tattare da ayyukan gidan Ali. Kuma tsarin Abbasiyawa mai mulki yana fahimtar muhimmiyar rawar da wancan aikin ulmi zai iya takawa ta bayan fage.
|