Jagorancin Imam Sadik (a.s)Daga cikin dubban masu da’awar shi’a a zamanin Imam Sajjad (a.s) mutum uku kadai suka rage bisa tafarki, mutum uku ne razanarwar Ummayawa da kamun da hukuma ke yiwa mutane bai sa su firgita ba, kuma son kubuta daga neman zaman lafiya bai girgiza azamarsu ba. Sun ci gaba da amsa kira da fama bisa wannan tafarki da cikakkiyar azama da tabbata. Guguwar da ta kwashi al’umma tamkar wasu zauna gari-banza suka kuma bi manufar azzalumar hukuma, ba ta kwashi wadannan mutanen ba. Dayansu watau Yahya ibn Ummi Dawil ya Wannan musulmi mai wilayar gaskiya ga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a) watau Yahaya bn Ummi Dawil, da wannan kiran nasa ya baiyana rabewa tsakanin masu gamsuwa da wilayar da ta takaita ga motsin rai alhali suna kwanto cikin abubuwan amfanin kansu, suna nitse cikin dattin kuntataccen zatinsu,da masu lizimtar Imam a tunani da kuma aiki. Bisa dabi’a wannan rabewa tana nufin wuce gaban cewa batattun masu rinjaye su janye mutum, amma ba tana nufin watsi da batattun ba. Da wannan fikira ne wannan salihar jama’a ta fuskanci aikin tsamar da duk wani mai iya ‘yantuwa daga wahala da kangi. Sannu a hankali, sai wannan jama’a mai jihadi da dauriya ta yawaita, kuma da wannan ne Imam Sadik (a.s) yake ishara yayin da ya ce: “…… daga bisani sai mutane suka dawo suka yi yawa†Ta haka ne Imam Sajjad ya ci gaba da ba da himma Ban ga wani bayyanannen sa-in-sa da hukuma a rayuwar Imam Sajjad (a.s) ba. Kamar yanda muka ambata, hakan shi ne abin da ya dace da hikima. Domin da ya dauki irin matsayin da muke gani a rayuwar Imam Musa ibn Ja’afar (a.s) da imaman da suka biyo bayansa dangane da mahukuntan zamaninsa da bai iya ciyar da aikin sauyi gaba har ya samar wa Imam Baqir (a.s) damar mayalwacin aiki ba. Da yayi haka da an hallaka shi da salihar jama’ar da take tare da shi. Ba mu iya tsinkayar ra’ayin Imam na hakika dangane da masu iko illa nadiran, ko a nan ma bai kai matsayin fito-na fito ba. Iyaka dai yana tabbatar da wani matsayi wa tahiri yana kuma fadakar da jama’ar da take kusa da shi Saboda haka takardar Imam tana bayyana matsayinsa Akwai kuma wasikar da Imam ya aikewa Abdulmalik ibn Marwan a matsayin jawabi A jawabin da ya rubuta, Imam ya baiyana ra’ayin musulunci a Ya ce: “ Babu karanta ga musulmi, karantar jahiliyya ce kawai karantaâ€. Da halifa ya karanta kalmomin Imam (a.s) ya fahimci ma’narsu,cikakkiyar famta,kamar yanda dansa Sulaiman ya tsinkayi ma’anar yayin da ya ce da mahaifinsa: “Ya Shugaban Muminai alfaharin da Ali bn Hussaini ya yi hakika ya yi tsanani!†Saboda gogewarsa ta siyasa,halifa sai ya amsa wa dansa da abin da zai nuna masa cewa ya fi shi sanin abin da karo da imamin shi’a zai hafar. Ya ce da shi: “Da na kada ka fadi haka,domin wadannan harsunan Bani Hashim ne masu tsaga dutse, masu kamfata daga teku. Da ma ai Ali ibn Hussaini yana bayyana daukakarsa a yanayin da sauran mutane suke fankamar mika wuya.†Wani misali mai nuna matsayin da Imam ya dauka shi ne yin watsi da wata bukatar Abdulmalik bin Marwan. Abdulmalik ya sami labarin cewa akwai takwabin Manzon Allah (s.a.w.a) wurin Imam sai ya aiko yana neman ya ba shi kyautarsa ya kuma yi barazanar yanke abin da ake baiwa Imam daga baitul mali.Sai Imam (a.s) ya rubuto masa:-
|