Jagorancin Imam Sadik (a.s)DUBI BIYU KARKATATTU Godiya tabatta ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da alayesa da wadanda suka yi koyi da shiriyarsu. Akwai karkatattun dubi guda biyu DUBI NA FARKO:- Ra’ayi ko kuma kallo irin na masu karewa watau masoya, wannan ra’ayin wasu masu zaton su mabiyan Imam Sadik (a.s) ne amma shi’arsa ne da fatar baki kawai banda aiki. Ra’ayin a takaice shi ne:- Cewa Imam Sadik (a.s) ya sami yanayin da imaman da suka gabace shi ko suka biyo bayan shi basu samu ba, yanayin da ya ba shi damar yada hukunce-hukuncen addini da kuma bude wa dalibai kofofin majlisinsa. Ya zauna gidansa yana karbar masu zuwa, ya rungumi karantarwa da yada ilmomi, duk dalibi ko mai bidar gaskiyan da ya zake masa yana kashe kishinsa na ilmi. Mutum dubu hudu suka yi karatu a gabansa, kuma ta hanyar wadannan dalibai ilmomin Imam Sadik sun watsu a ko ina. Daga cikinsu akwai ilmomin addini kamar su fikihu da hadisi da tafsiri, akwai kuma ilmomin dan’adamtaka kamar su tarihi da kyawawan dabi’u da ilmin zamantakewar al’umma. Imamu ya yi mukabala da ma’abota sababbin ra’ayoyi, ya yi raddi Ma’abota wannan mahanga suna karawa da cewa: domin burin Imam a kan ci gaban wannan gagarumin aikin ilmantarwa, dole ta sa ya guji sa baki cikin al’amuran siyasa, saboda haka bai gabatar da kowani aikin siyasa ba, bugu da kari ya ma zabi hanyar daidaitawa da irin siyasar halifofin zamaninsa domin dadada musu da nisantar duk wata rikitarwa da ka iya kusantar aikinsa. Don haka bai yi fito-na-fito da halifofin ba, ya kuma hana kowa yin hakan. Wani zubin ma yanayi yana sawa Imam ya je gaisuwa ya kuma sami kyaututtuka da goyon bayansu. Idan shugaba ya yi masa mummunan zato sakamakon faruwar wata harkar tawaye ko kuma tsegunta masa wata tuhuma, Imam ya Ma’abotan wannan dubin su Wannan ra’ayi yana sifanta Imam da cewa shi masani ne mai bincike, Abu Hanifa da malik sun sha daga kogin ilminsa, sai dai ya yi matukar nisantar yaki da zaluntar addini da masu mulki ke yi, ya kuma nisanci bukatun umurni da kyakkyawan aiki da hana munkari yayin da sarki ya zama ja’iri. Imam ba shi da wata dangantaka da masu tawaye wa zalunci ire-iren su Zaid ibn Ali da Muhammad bn Abdullah da Hassan bn Ali shahidin Fakh ko kuma rundunonin wadannan mutane. Bai kasance yana mai da martani kan abin da yake aukawa jama’ar musulmi, ko nuna damuwa kan dimbin dukiyar da Mansur yake tarawa, ko yunwar da ‘ya’yan Annabi (s.a.w.a) suke fama da ita a cikin tsaunukan Tabaristan da Mazandaran da garuruwan Irak da Iran ba, ta yanda basu da abinda zasu sa a baka ko abinda zai rufe musu al’aura idan suna son salla a jam’i !! Kuma ba ruwansa da kisa da azabtarwa da tarwatsa mabiyansa alhali suna hannu rabbana basu samun ko da kwatankwancin abin da marasa galihun wancan lokaci suke mora!!!
|