Jagorancin Imam Sadik (a.s)



A cikin littafin (babi) Alhujja na Alkafi akwai wani hadisi wanda aka ruwaito daga Imam Ali ibn Musa Alrida(a.s) ya ambaci abin da ya danganci sanin imam da sifofinsa, filla-filla, bayanin da ya kunshi ma’anoni masu zurfi da gwanin kyau.

Daga wadannan  riwayoyi akwai wadanda suka bayyana imamanci da cewa: “Shi matsayin anabawa ne, gadon wasiyyai. Sannan dai imamanci halifancin Allah ne kuma halifancin Manzo ne,mukamin Amirul muminina (a.s) ne, gadon Hassan da Hussaini (a.s)ne. Sannan kuma imamanci ragamar addini ne,dadaiton musulmi ne, kyautatuwan duniya ne, daukakar muminai ne. Shi imamanci ginshikin musulunci ne mai yado da  albarka, reshensa ne mai daukaka. Da  imami ne salla da zakka da azumi da haji da jihadi suke cika, da  shi ne ake samar da ganima ( fai’i) da sadakoki da zartar da haddodi da hukunce-hukunce da kare iyakokin kasa”[28]

 

A kan imami kuma cewa ya yi:-

“(Shi) tauraruwa mai shiryarwa ne, ruwan dadi ne,  matsera daga halaka ne, girgije mai kawo ruwa ne, mafakar bayi a lokacin bala’i ne, amintaccen Allah kan halitarsa ne, hujjarsa bisa bayinsa ne, halifansa a kasashe ne, mai kira zuwa ga Allah, mai tsare hurumin Allah ne, daidaiton addini ne, daukakar musulmi ne, fushin munafukai ne, kuma halakan kafirai ne”[29]

Duk nauye-nauye da mas’uliyyar da Annabi ya gudanar, Ali (a.s) da imamai daga ‘ya’yansa suna  daukarsu.[30]

A wata riwaya daga Imam Sadik (a.s) akwai ta’kidi kan biyayya ga ‘wasiyyai’.  Riwayar ta fayyace cewa wasiyyan su ne wadanda Alkur’ani ya kira da lakabin ulul amri .[31]

Daruruwan riwayoyi da ke rarrabe cikin babi daban-daban suna fayyace mana cewa manufar imam da imamanci a tunanin shi’a ba komai ba ce face jagoranci da gudanarwa na al’amuran musulmar al’umma kuma imaman Ahlulabaiti (a.s) basu  takaita wajen da’awar imamanci kan abin da ya shafi  tunani da ma’nawiyya kadai ba, a’a suna kira da cewa hukuma ita ma tasu ce. Kiransu mai fadi kamar haka mai kuma tattara dukkan sassa hakika kira ce ta wata harakar siyasa da kuma soji wadda take da zimmar karbar shugabanci.

Wannan batu ya ci gaba da zama boyayye ga masu bincike a zamunnan da suka biyo baya amma a fahimtar sahabban imamai da wadanda suka yi zamani da su batun yana daga mafi bayyanannun al’amura. A cikin daya daga kasidunsa na Hashimiyyat, Kumait yana sifanta imaman Ahlulbaiti da cewa su ne shugabanni masu jagorantar mutane ta wata hanya wacce ta saba gaba daya da hanyar da azzaluman mahukunta suka bi, inda suke mu’amala da mutane tamkar dabbobi.[32]

Mu koma ga maudu’in asali cewa kashin baya a kiran Imam Sadik (a.s) da sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) shi ne batun imamanci. A tare da mu akwai riwayoyi masu karfafa juna wadanda suke tabbatar da wannan batu na tarihi. Ana nakalto su a bayyane tare kuma da wannan fayyacewa daga Imam Sadik (a.s) inda ya yi da’awar imamanci. Za mu bayyana  nan gaba cewa lokacin da Imam yake bayar da sanarwar wannan kiran  nasa, yana ganin kansa cikin wani mataki na jihadi mai bukatar ya yi watsi da mahukuntan zamaninsa, ta hanya bayyananna kuma kai tsaye, sannan kuma ya sanar cewa shi ne ma’abocin hakki na hakika, ma’abocin shugabanci (wilaya) da kuma imamanci. Irin wannan fitowa, bisa al’ada, tana nufin an ketare sauran matakan jihadi wadanda suke gabatarta tare da nasara. Dole ne ya kasance farkawa a siyasance da yanayin zaman jama’a ta zama tuni ta sami goyon baya mai fadi, ana jin shirin mutane ya yi karfi a ko wani wuri, shimfida kan manufa ta kankama ga wani adadin mutane mai dama, sannan jama’a masu yawa sun yi imani da wajibcin kafa hukumar gaskiya da adalci, sannan daga  karshe, jagoran ya zama ya riga ya dauki kuduri mai karfi akan wannan fito-na-fito mai tsanani. Idan wadannan sharuddan basu cika ba,sanarda imamancin wani mutum ayyananne da jagorancin sa na gaskiya  ga al’umma abu ne mai tattare da ujula ba kuma cimma manufa tare da shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next