Jagorancin Imam Sadik (a.s)Yanayin da ake ciki da shirin da ayyukan imamin da ya gabata (Imam Bakir) bai shafi takwabi ba. A’a shi yana tsayawa ne ta hanyar suka mai tsanani, sawa’un da salon aikin gyaran tunani ko na tsare-tsare ko kuma ta wata fuskar dabam, da nufin kwankwasar azzalumai da yakar su. A nan Imam Bakir (a.s) yana karfafawa La’alla wadannan fayyace-fayyacen Imam Bakir su ne suka yada tunanin yunkurin Imam Sadik (a.s) da halifancinsa a tsakanin ‘yan shi’a, ya kuma sanya sahabban Imam Bakir da Imam sadik(a.s) sauraron wata faraga daga lokaci zuwa lokaci. Akwai wata riwaya cikin Rijal na Shaikh Kashshi wacce a cikinta ana iya fahimtar wannan yanayi mai wanzuwa a tsakanin mabiya Ahlulbaiti a wancan lokacin. Ibn Miskan ya ruwaito daga Zurara cewa ya tambayi Abu Abdillah (a.s) batun wani mutum cikin abokanmu wanda yake buya saboda gudun Kalamar ‘wannan al’amari’ a sanin mabiya Ahlulbaiti kinaya ce A wata riwaya Hisham Ibn Salim wanda shi ma wani babba ne kuma sananne daga cikin shi’a, ya ambaci cewa Zurara ya ce da shi: “Ba zaka ga wani Daga jumlar abin da ya gabata muna fahimtar cewa a ra’ayin babansa da na jama’a Imam Sadik (a.s) shi ne mai tabbatar da burin imamanci da shi’anci. Kuma silsilar imamanci ta Tun lokacin da ya karbi nauyin shugabaci har zuwa wafatinsa, Imam ya dauki shekara talatin da uku yana jihadi maras yankewa. Cikin wadannan shekarun yanayi ya kasance yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana hawa da kuma sauka;wani zubi ya dace da maslahar mazhabin Ahlulbaiti, wani zubin kuwa yanayin ya juya akasin hakan. Wani lokaci halin yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana tsanani, har sahabban Imam su zaci cewa dukkan buri ya tarwatse. A duk wadannan halaye Imam Sadik(a.s) yana rike da ragamar jagoranci kyam tare da azama da jajircewa. A nan ya zama wajibi mu yi nuni da wani al’amari mai ban takaici wanda dukkan masu bincike Wannan kuwa shi ne halin rashin tabbas wanda ya lullube shekarun farkon imamanci Sadik(a.s) wadanda suka yi muni daidai da karshen zamanin Banu Umayya. A lokacin rayuwa ba ta san natsuwa ba tana kuma cike da aukuwar manya-manyan al’amura,muna iya fahimtar alamunsu cikin daruruwan riwayoyi. Sai dai malaman tarihi da hadisi basu kawo mana labarin wannan lokacin a jere tare da sajewa da daganta wannan bayani da wancan ba. Saboda haka ya zama dole ga mai bincike ya yi dogaro da kuma lura da al’amura da suke baiyana cikin abinda yake karantawa (kara’in), ya lura da kungiyoyi da ra’ayoyi a game na wancan zamani sannan ya kwatanta ko wace riwaya da bayanan da ya riga ya sani domin ya ga abin fahimtar(mafhumi) abinda riwayar ta kunsa da rabe-raben ta. La’alla daya daga dalilan wannan rikitarwa shi ne kasancewa harakar Imam da mabiyansa an yi ta cikin sirri, domin shiri na siri wanda ya kafu bisa ingantattun ginshikai dole ne bayanan da suka dangance shi su wanzu cikin sirri da boyewa, kuma wajibi ne kada wanda yake waje da wannan shiri ya tsinkaye su. Wadannan bayanai ba su watsuwa sai bayan tabbatar harakar da kuma nasararta. Saboda haka ne muke samun cikakkun bayanai dalla-dalla Akwai wani dalilin daban wanda zai iya janyo wannan rashin baiyana dangane da harakar Ahlulbaiti, cewa murubuta tarihi, bisa al’ada suna rubuta abin da yake dadada wa sarakuna ne. Domin haka muke ganin bayanai filla-filla kan rayuwar halifofi da wasanninsu da hirarrakinsu da wuraren holewarsu amma bamu ganin bayanan kirki kan masu neman juyi da wadanda aka zalunta da wadanda aka murkushe. Domin samun irin wadannan bayanan mai bin diddigi na bukatar dogon bincike da kirkado da tsananin biyawa. Amma rayuwar halifofi bayani ne tanadadde, tsuntsu daga sama gasashshe, yana kawo yardarsu da tarin kyaututtuka.
|