Gudummawar Mace"Lalle ni ina kin namiji ya kamantu da mace'. [5]Ma'anar `ki' a nan shi ne haramci da rashin halalci, kamar yadda ya zo a sunan babin. Haka nan an ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana tsawatar da maza kar su kamantu da mata, yana kuma hana mata kamantuwa da maza cikin suturarta".[6] An karbo daga Ibin Abbas ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana tsinewa mazan da ke kamantuwa da mata, da matan da ke kamantuwa da maza.[7] Fayyace wadannan bambance-bambance zai haifar da amincewa a ilmance da bambance-bambancen ayyuka a wasu fagage da wajiban da aka kallafawa kowane daya daga namiji da mace. Daga wannan asasi ne bambance-bambance da inda ake tare cikin ayyukan zamantakewa ke iyakantuwa. MACE DA WAYEWAR DUNIYANCI Karanta tarihin al'ummu da kasashe a tsawon zamunansu, yanafito mana da wahalhalun mace, kuntata mata da takura mata. Babu wani tsari ko akida da ya yaye wa mace mayafin zalunci da kuntatawa in ba ka'idojin Allah da suka hadu da mafi kyawun surarsu a sakon Musulunci madawwami ba. Kafin mu bayar da bayani game da kimar mace, hakkokinta da matsayinta mai ban sha'awa a Musulunci, yana da kyau mu kawo wasu alkaluman kididdiga wadanda ke magana a kan wahalhalun mace da masifun da ta sha a karkashin wayewar duniyanci na zamani karkashin jagorancin Amirka da kasashen Turai, wadanda ke daga taken 'hakkokin mace'. Alkaluman kididdiga na ta'akidi a kan cewa, dan Adam din da ya ji jiki a karkashin wannan wayewa, kuma ya zama bawa da na'urar jin dadi shi ne: Mace. Ga wasu daga cikin alkaluman kiddidiga na cewa:
|