Gudummawar MaceShiri da tarbiyya na da tasiri mai karfi wajen gini da hada mutum da aikinsa a cikin al'umma, da fuskantar da iyawarsa da kokarinsa zuwa mafuskanta ta gini mai kyau. A halin yin watsi da mutum da hana shi tarbiyya da fuskantarwa, da tanaji mai tsari kuwa, zai sa ya tashi sakakke, wanda yanayi da fare-fare ke galaba a kan shi, irin wad'anda a galibi suke musabbabin lalacewar mutum da tafiyar kokari da kwarewarsa da yi wa ci gaban zamantakewa tangarda; daga nan sai mutum ya zama mai rauni sukurkutacce, baya iya mu'amala da al'umma da fare-fare da matsaloli da damammaki da mu'amala mai nasara. Surar nan ta misali a Musulunci wadda ya wajaba ta yi nazarin yanayin mace ta hanyar ta, ita ce surar mace a cikin AIKur'ani da sunna, wadda kuma ke tsaye a kan asasai masu yawa kamar haka: 1-Kadaitar Nau'in dan Adam: Wadda ta ginu a kan asasin fadar Allah Madaukaki: "Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, wanda Ya halicce ku daga rai guda daya (Adamu), Ya kuma halittar masa mata (Hauwa'u) daga gare shi, Ya kuma baza maza da mata masu yawa daga gare su. Ku ji tsoron Allah Wanda kuke tambayar (taimakon junanku) da Shi, kuma (ku ji tsoron hakkokin) zumunta. Hakika Allah Ya kasance Mai kiwo ne a gare ku". Surar Nisa'i, 4:1. Muna iya fahimtar cewa girman wannan aya ba kawai daga abin da ta kunsa na manyan ma'anoni ba ne, a'a har ma daga bude Surar Nisa'i, wadda ke magana game da sha'anonin mata, da wannan aya; wadda kuma take cikin manyan surori, da d'aukar wannan aya a mastayin asasi da mabubbugar tunani da shar'ancin Musulunci wadanda suka tsara alaka tsakanin namiji da mace, suka kuma iyakance matsayinta da gudummawarta a cikin al'umma. 2-Asasi na biyu da ya wajaba a yi nazarin shi a bisa asasin alaka tsakanin namiji da mace shi ne alakar so, kauna, tausayi, tabbaci da natsuwar zuci, wad'anda suka misaltu a fadar Allah Madaukaki: "Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 30:21. 3- Daidaitawa cikin hakkoki da wajibai: "..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228. Wannan yana nufin cewa kowane daya daga namiji da mace akwai hakki na wajibi da ya hau kanshi kuma ya zama wajibi ya aiwatar da abin da ya hau kanshi game da dayan da kyautatawa da zamantakewa mai kyau. Da wannan Musulunci ya auna kuma ya tsara a sasan alaka da wannan ka'ida ta shari'a da halayya makadaiciya, sai ya tabbatar da mafi daukakar ka'ida ga hakkin mace.
|