Gudummawar MaceA sakamakon bunkasar bukatun mutum da al'umma, da sabanin daidaikun mutane daga maza da mata wajen kudura da iyawa ta hankali da jiki da rai; da karfin irada, sai kebance aikin kowa ya faru a cikin al'umma a hankali a hankali ta wata fuska, ta wata fuskar kuma tare da zabin mutum ga aikinsa na zamantakewa, wato nau'in aikin da zai yi cikin al'umma, kamar noma ko aikin likita ko kasuwanci ko karantarwa da wasun su, ko wani mai tsare-tsare daga gwamnatin Musulunci, ta fuska ta uku, wato wanda nauyin tsara al'umma da fuskantar da kudurarta ke wuyansa, don biyan bukatun daidaiku da magance matsalolin da ke samo asali daga bukatu daban-daban. Cikin abin da zai zo za mu yi nazari gudummawar mace a wadannan fagage, mu dan yi bayani a kansu ko da kuwa a takaice ne. BAMBANCE-BAMBANCEN YANAYIN HALITTA DA KE TSAKANIN NAMIJI DA MACE Daya daga cikin mas'alolin ilimi da kowa ya mika wuya garesu a tsakanin masana halayyar dan Adam da likitanci, shi ne cewa kowane daya daga namiji da mace na da yanayin halittarsa ta kebanta da shi, da cewa a dabi'ance dole a sakamakon haka ayyukan mace a cikin rayuwar zamantakewa ya saba da na namiji. don haka daidaitar rayuwar zamantakewa na bukatar kowane daya daga namiji da mace ya kiyaye bangare da yake ciki na jinsi, namiji ya kiyaye mazantarsa mace kuma ta kiyaye matancinta. Hakika AIkur'ani mai girma ya yi bayanin bambanci halitta da ke tsakanin jinsosin nan biyu, abin da ya haifar da bambancin ayyuka, haka nan ya bayyana inda jinsosin biyu suka dace, Allah Madaukakin ya ce: "Kuma kar ku yi burin abin da Allah Ya fifita wasunku da shi a kan wasu. Maza na da sakamakon abin da suka aikata, haka ma mata suna da sakamakon abin da suka aikata. Kuma ku roki Allah daga falalarSa, hakika Allah Ya kasance Masani ne da dukkan komai". Surar Nisa'i, 4:32. Haka nan hadisai sun yi ta'akidi a kan cewa mabayyanar kamala cikin mutuntakar kowane daya daga namiji da mace, suna da alaka da irin kebance-kebancen nau'i ga kowane daya daga cikinsu, da kiyayewarsa a kan su da daukakarsa da su, don haka hadisai suka hana kamantuwar mata da maza, kamar yadda suka hana maza ma hakan. Darussan halayyar dan Adam da gwaje-gwajen da aka gndanar <ta wasu halayyar karkacewa a wajen bangarorin biyu, sun nuna cewa karkatar wasu mazaje zuwa kamantuwa da mata da karkatar mata zuwa kamantuwa da maza shi ne halin lalacewa ; da cewa ana iya shawo kan irin wannan halayya a rnagance ta ta hanyar tarbiyyar yanayin zamantakewa da sake tsara mutuntaka. A cikin hadisai akwai hani da tsawatarwa masu tsanani a kan irin wannan hali, kai! har ma sun la'anci irin mutane masu wannan hali. Babban malamin hadisin nan kuma masanin furu'a Hurrul Amili (Allah Ya rahamshe shi) ya kawo hadisai masu yawa karkashin babin `Rashin halaccin kamantuwar mata da maza da maza da mata'. An ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) da Imam Ridha (a.s.) cewa: -
|