Gudummawar MaceHakika shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki, ta kuma karakwadaitarwa a kan shi da abin da ba ya bukatar kari a cikin nassosi da karantarwa da matsayi na aikace. Daga cikin su akwai fadar Allah Madaukaki: " (Allah) Shi ne Wanda Ya sanya kasa horarriya, saboda haka ku yi tafiya a cikin sassanta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma makoma zuwa gare Shi ne (kawai)". Surar Mulki, 67:15. Haka nan akwai fadarSa Madaukaki: "Sannan idan aka idar da Salla, sai ku bazu cikin kasa ku nemi falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa tsammaninku ku rabauta". Surar .Tuma'ati, 62:10 Haka nan akwai fadarSa: "Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka, kuma kar ka manta da rabonka na duniya..". Surar Kasasi, 28:77. Kamar yadda shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki da neman kudi, haka ta yi bayani a kan bambamce-bambamcen karfi da iyawar dan Adam, da wajibcin samun kamala ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaikun nau'in dan Adam; Allah Madaukaki Ya ce: "...kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hldima." Surar Zukhrufi, 43:32. Kamar yadda AIkur'ani ya kwadaitar a kan yin aiki,neman abinci da musayar amfanoni; Manzon Allah (s.a.w.a.) na daukar yin aiki da neman arziki a matsayin jihadi da ibada; hakika haka ya zo cikin abin da aka ruwaito daga gare shi (s.a.w.a.) cewa: "Mai wahalar neman kudi don iyali kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah".[18]
|