Gudummawar MaceGINA AL'UMMA TA HANYAR ALAKOKIN IYALI Ta bayyana gare mu cewa al'umma na tsayuwa ne a kan asasai uku kamar haka: 1-Tasiri tsakanin halayyar nan ta mace da namiji da siffofin da kowannensu ke da shi na jiki da rai, da cewa jin dadin al'umma da amincinsa na rai da bunkasar zamantakewa da bukatun rayuwa da fadadar hanyoyin shiga da daidaiton halayyar su, duk suna da alaka mai nisa ta hanyar daidaitaccen tasirin da ake musaya tsakanin jinsosin biyu, wato jinsin namiji da jinsin mace. 2- Alakar tunani da wayewa da suka hadu a kai. 3- musayar amfanoni tsakanin daidaikun al'umma mazansu da matansu. A kan asasai na daya da na uku ne ayyukan zamantakewa ga kowane daya daga daidaikun al'umma mazansu da matansu ya samo asali, kowanne da yadda ya dace da karfinsa na jiki da hankali da kuma inda ransa ya fi karkata. Daga nan ne mace ke motsawa don tarayya cikin aikin gina gida da al'umma, kuma mafi fadin fagagen wannan tarayya shi ne fagen iyali. Hakika sakamakon darussan kan halayyar dan Adam sun isa zuwa ga abin da Alkur'ani mai girma ya bayyana, na cewa iyali shi ne ginshikin ginin al'umma, kuma tushe da asasi daga muhimman asasan da ake gina rayuwar al'umma a kan su; don haka AIkur'ani ya bayyana haka, ya kuma sanya ka'idojin alakar auratayya, ya bayyana hakkokin da wajiban da ke kan kowane daya daga namij da mace, don su iya aiki da gina rayuwar zamantakewa mai lafiya. "Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lallai cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu, 30:21. "Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai daya (wato Annabi Adamu), Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita.." Surar A'arafi, 7:189. "Maza sama suke da mata saboda abin da Allah Ya fifita sashensu (da shi) a kan sashi, da kuma abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu. Sannan mata na gari masu biyayya ne (kuma) masu kiyaye asirin abin da ke boye wanda Allah Ya kiyaye..." Surar Nisa'i, 4:34.
|