Gudummawar MaceAbin da muka gabatar na alkaluman kididdiga suna magana a kan karkacewar jima'i saboda wasu dalilai na ayyuka da Alkur'ani ya yi bayaninsu ga mutane ya kuma tsawatar a kansu. 4-Mugun kulli na gado da tsoron Musulunci: Daga cikin sabubban kai hari ga Musulunci da yi wa matsayinshi game da mace bakin fyanti, akwai mugun kullin da aka gada a kan Musulunci da yin aiki wajen munanta ka'idojinsa da daukakan halayensa tun daga bayyanar Manzon Allah (s.a.w.a.), wanda kuma ya ci gaba har zuwa yakokin gicciye. Duk wannan saboda tsoron Musulunci a matsayin shi na wani shiri na wayewa wanda ke rushe amfanoninsu da suka haddasa, kuma ba su gushe ba suna haddasawa a duniyar Musulunci, kuma yana gamawa da wuce-iyakarsu da mamayarsu ga duniya, masamman ma duniyar Musulmi; masamman bayan bayyanar wayewar Musulunci da bayyanar Musulunci a matsayin wani shiri da yunkure-yunkurenshi ke ginuwa, kuma wani rayayyen gwajin da ya aikatu ta hanyar tsayar da gwamnatin Musulunci a Iran. Hakika kuwa manyan kasashen duniya sun watsa karti datsare-tsarensu, suka watsa'yan barandansu a ko'ina don yaki da wayewar musulunci, da sukar shirinshi da masu kira zuwa gare shi da wadanda ke dauke da tutarsa. MACE A RAYUWAR ANNABAWA (A.S.) Hakika mace ta kasance tana da babban kashi hayyananne a tafiyar kira zuwa ga Allah da yunkurin Annabawa da Manzanni (a.s.). Hakika mace ta taka muhimmiyar rawa wajen yakin tunani da siyasa, ta kuma sha azaba, kisa, hijira da dukkan nau'o'in wahalhalu da ta'addancin tunani, siyasa da fin karfi. ta kuma mike ta bayyana ra'ayinta bisa 'yanci, ta shiga cikin kira zuwa ga Allah, duk kuwa da abin da ya same ta na hasarar mulki, matsayi da dukiya; da abubuwan da ta hadu da su na kora, kisa da ta'addanci. Misali a kan haka ita ce Maryam Uwar Annabi Isa (a.s.), wadda AlKur'ani ya girmamata kamar yadda Annabin Musulunci (s.a.w.a.) ya girmamata. Hakika Alkur'ani, a ayoyi masu yawa, ya yabi wannan mace abin koyi, ya kuma kaddamar da ita a mastsayin wata abin koyi ga maza, kamar kuma yadda ya gabatar da ita abin koyi ga mata don su yi koyi da dabi'unta da daidaiton tunaninta da mutuntakarta. Duk wanda ke karanta tarihin mace cikin da'awar Allah, zai same ta ana magana da ita kamar yadda ake yi da namiji, ba tare da maganar Allah ta nuna wani bambanci tsakaninsu ba saboda kasancewa namiji ko mace. Ta hanyar nazari tarihin rayuwar mata cikin tafiyar kira zuwa ga Allah, za mu iya fahimtar matsayi na ja-goranci da tasiri da mace ta samu a rayuwar Annabawa da kiraye-kirayensu, da haka kuma kimar mace a cikin al'ummar Musulmi da shigar ta cikin harkokin siyasa, da hakkokinta na mutuntaka da doka, za su bayyana. Za mu ga irin wannan tarayya mai fadi idan muka karanta kissar gwagwarmayar uban Annabawa Ibrahim (a.s.) da mutanensa a Babil da ke kasar Iraki, da fito-na-fitonsa da Namarudu, fito-na-fiton nan da ta kare da tsirar Annabi Ibrahim (a.s.) daga wuta ta hanyar mu'ujizar Allah wadda tafi karfin tunanin hankali na zahiri. kumaal'amarin da ya sa shi (Annabi Ibrahim) yin hijira zuwa garin Sham. Matarsa Saratu wadda ta yi imani da kiransa ta kasance abokiyar jihadinsa.wadda ta kasance tare da shi a lokacin hijirarsa zuwa Sham. daganan zuwa Masar. kuma ya sake dawowa Sham ya zauna a can. inda wani babban zango daga zangogin tarihin dan Adam ya fara a hannun Annabi Ibrahim (a.s.) alhali matarsa Saratu na tare da shi, tana tsaye a gefensa cikin jihadinsa, wahalhalunsa da hijirarsa. Alkur'ani mai girma na magana game da kissar hijira da rayuwar wannan iyali, kamar yadda yake magana game da gudummawar matar Ibrahim (a.s.) ta biyu, da shigar ta wajen rubuta littafin wannan zango mai haske a tarihin mutum a kasar Hijaz, a garin Makka mai girma wanda ya iso shi yayin da ya baro Masar. Hakika kissar wannan mata na daga mafi shaharar kissoshin tarihi kuma wadanda suka fi ban mamaki kuma suka fi girman gwagwarmaya da hakuri. domin ta ta'allaka a saman tarihi ta hanyar renon dan Annabi Isma'ila (a.s.) a wani kwari da baya shukuwa a wajen Daki mai alfarma, don ya zama uba ga mafi girman Annabawa a tarihin bil Adama, wannan shi ne Muhammadu (s.a.w.a.); Alkur'ani na bayyana wannan al'amari da cewa:
|