Gudummawar Mace"..kuma suna da hakkoki a kan mazajensu kamar (yadda mazajensu ke da hakkoki) a kansu da kyautatawa.." Surar Bakara, 2:228. "..Kuma ku zauna da su da kyautatawa.." Surar Nisa'i, 4:19. "Kuma ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa.." Surar Dalaki, 65:7. "Kuma ku taimaki juna da aikin alheri da tsoron Allah, kuma kar ku taimaki juna a kan yin sabo da ta'adda.." Surar Ma'ida, 5:2. Haka nan kamar yadda AIkur'ani mai girma ya yimagana game da asasai da alakokin `yan Adamtaka da doka a iyali, haka nan ma hadisan Annabi suka yi magana a kan haka, za mu ambaci abin da aka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.): "Dukkan ku masu kiwo ne kuma wadanda za a tambaya a kan kiwonsu; sarki da ke saman mutane mai kiwo ne kuma abin tambaya a kan abin da yake kiwo, namiji mai kiwo ne a kan iyalinsa kuma shi abin tambaya ne a kansu; mace mai kiwo ce a kan gidan mijinta da `ya'yanshi kuma ita abar tambaya ce a kansu, bawa mai kiwo ne a kan dukiyar ubangidansa kuma shi abin tambaya ne a kan shi. Ku saurara, dukkan ku masu kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne a kan abin da yake kiwo."[16] Da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) cewa:"Daga cikin dabi'un Annabawa akwai son mata". Da abin da aka ruwaito daga gare shi (a.s.) cewa:"Bana tsammanin mutum na kara alheri a kan imani har sai ya kara so ga mata.[17] Yana da kyau a nan mu yi ishara da cewa ginin da mace ke yi a cikin al'umma a wasu lokuta ya kan zama aiki ne kai tsaye, a wasu kuma ya kan zama ta hanyar alakarta ta rai da halayya da miji da `ya'ya. Matar da ke samarda yanayin hutawa da kyakkyawan zamantakewa da miji, take kuma tabbatar da kauna, soyayya da kwanciyar hankali, kamar yadda ya kamata a alakokin da ke tsakaninsu, to irin wadannan yanayoyi na rai suna tasiri ga miji da alakarsa ta zamantakewa da wasu, da ikonsa na neman abinci da bayarwa. wannankuwa saboda yanayin rai ga mutum yana tasiri a daukacin harkokinsa da alakokinsa da wasu. Amma lokacin da rayuwar aure ta cika da matsaloli da damuwa da tashe-tashen hankula, to wannan yana tasiri mara kyau ga miji, aikinsa, neman abinci da alakokinsa da wasu. Kamar yadda yanayoyin rai a cikin iyali ke tasiri ga miji, haka yake tasiri ga `ya'ya; domin yaron da ya tashi cikin yanayin kiyayya, rikice-rikce, matsaloli da mummunan mu'amala, da wuya ya zama daidaitaccen mutum cikin halayyarsa da alakokinsa da wasu, da fuskantar da iyawarsa ta tunani da jiki; domin so tari yaro, saboda yanayin mummunar tarbiyya, yakan sauya ya zama karkataccen mutum mai adawa, ko malalaci da ba ya amfanin komai, ko birkitacce mai kawo matsaloli da aikata laifuka. Alhali kyakkyawar tarbiyya na taimakawa wajen samar da mikakken mutum, ta yadda irin wannan tarbiyya ke tasiri a rayuwar gobe ta yaro ta ilimi, zamantakewa da tattalin arziki. Don haka gudummawar mace ke da tasiri wajen ginin zamantakewa ta hanyar tarbiyya da tanajin ingantattun mutane ga al'umma; haka nan ta hanyar samar da yanayi mai kayu ga miji. A cikin wadannan nassosi Akur'ani mai girma da hadisai masu tsarki sun iyakance asasai da ka'idoji na dokokin, halayya, tarbiyya, tsari da gudanar da iyali; a kan wannan hanya kuma mace na taimakawa wajen ginin al'umma. Ginin al'umma kuwa ya ginu a kan asasai kamar.Soyayya da kauna da jin kai da girmamawa tsakanin ma'aurata.
|