Gudummawar Mace



Daga cikin wuraren da ake suka a cikin wannan rahoto akwai karuwar yawan kananan yara da ke rayuwa cikin halin talauci a Biritaniya, da karuwar alkaluman rabuwar aure, da raguwar tallafin hukuma ga matalautan iyalai, da karuwar yawan yara da samari da ke sake suna kwana a tituna.

Haka nan masu rubuta rahoton sun bayyana damuwarsu da mummunar mu'amala da amfani da miyagun kwayoyi da fyade da ke fuskantar kananan yara.

Kamar yadda majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana, rahotannin majalisar game da yanayi kananan yara a kasashen Sweden, Norway da Denmerk sun yi soke-soke kamar irin na rahoton kasar Biritaniya".

Haka nan ya zo cikin jaridar Jumhuri Islami, a adadinta na 4,485 cewa:­"Ofishin kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran a Born (ta fcasar Jamus) ya bayyana rahoton hukumar kidaya ta kasar Jamus (a shekara ta 1993) na cewa: adadin `ya `ya mata da ubanninsu ke tarbiyyantar da su su kadai yana ci gaba da karuwa a kowace shekara. Rahoton ya kara da cewa: A halin yanzu akwai kimanin uwaye mata dubu 455 a jihohin Jamus ta gabas (wato kashi 12 bisa (Tari na jimillar uwaye mata da ke wadannan jihohi ke nan) da ke tarbiyyantar da ya yansu su kadai. A gefen wannan kuma, daga uwaye mata miliyan 7 da ke jihohin Jamus ta yamma, kimanin dubu 915 (wato kashi 12 bisa dari) na uwaye matan suna daukar dawainiyar tarbiyyar 'ya `yansu su kadai. Da wannan ke nan zai zarna akwai kimanin uwaye mata miliyan daya da dubu 370 a tsakanin uwaye miliyan 9 da dubu 260 da ke tarbiyyar 'ya`yansu su kadai a tarayyar Jamus.

Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, kashi 46 bisa dari na wadannan uwaye a gabashin Jamus, da kashi 30 bisa dari daga yammacinta duk ba su yi aure na shari'a ba; kashi 43 bisa dari na wadannan uwaye kuwa mazajensu sun sake su, kasancewar kuma rike 'ya’ya a hannun uwaye mata yake, ya zama musu dole su dauki dawainiyar tarbiyyarsu.

Haka nan a kasar Jamus akwai fiye da uwaye mata miliyan 9.26 da suka haifi 'yaya alhali shekarunsu na haihuwa bai kai 18 ba, kuma miliyan 5.4 daga cikinsu ko da yaushe ko rabin lokutansu suna ayyuka ne a wajen gida, banda kuma ayyukansu na gida da ayyukan tarbiyyar yara. Wani abu da ya kamata a bayyana a nan shi ne cewa yawan halin rabuwar aure a halin yanzu ya ninka yadda ya kasance a shekara ta 1968, wato ya karu daga dubu 65 da ya kasance a shekara ta 1968 zuwa dubu 135 a â€کyan shekarun nan, kuma a kowace shekara ana rijistar aurarraki dubu 390 a kasar Jamus, wadanda kashi 33 bisa dari daga cikinsu ke karewa da rabuwa, har ma wannan adadin a manyan garuruwa irin Hanburg ya kai kashi 50 bisa dari".

Har ila yau jaridar Ittila'at a adadinta na 20,503 ta dauko wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillacin labaran Iran (IRNA) ya kawo kamar haka:­

"Taimakon kasar Amirka ga hukmar (UNICEF), bai kai na kasa daya daga cikin kasashe 20 masu arzikin masana'antu a duniya ba.Bankin kula da Kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ma ya tabbatar da haka, ya kuma kara da cewa: Duk da Amirka da ke bayar da taimakon dala biliyan 9.7, ita ke martaba ta biyu bayan Kasar Japan wajen taimakawa hukumar UNICEF, wannan adadin kudi kuwa ba komai ba ne face kashi .15 bisa dari din kudaden shiganta, alhali kuwa Rasar Holland da sauran kasashen yankin Sakandanebiya su ke marhala ta daya a wannan fagen; domin taimakonsu na kaiwa kahi 8 bisa dari na kudaden shigansu. Shugabannin hukumar UNICEF sun nuna damuwarsu a kan raguwar taimakon da kasashe masu zarafi ke yi ga matalautan kasashe, har ma sun kara da cewa: 'Wannan abu na faruwa ne a daidai lokacin da rnuhimmancin taimakawa wajen kyautata lafiyar Kananan yara da kyautata yanayin ayyukan uwaye mata ke Karuwa a matalautan kasashe da tsananin gaske kuwa.' Kuma kamar yadda wannan rahoton ya nuna, a kowace shekara Kananan yara kimanin miliyan 13 a duniya ke mutuwa saboda cututtukan gudawa, bakon-dauro da sauransu.Haka nan kimanin Kananan yara miliyan 200 ke fama da rashin abinci mai gina jiki irin su vitamin A, abin da ke haifar musu da makanta!".

Har ila yau ya zo cikin jaridar Ittila'at, a adadinta na 20,370, fitowar ranar 15 ga watan Disamban shekara ta 1994 cewa:­

"Kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran (IRNA) daga Tehran ya bayarda labarin samuwar kananan yara kimanin rabin miliyan wadanda suka tarwatse a Amirka, a wasu lokuta ana aje su a wajen neman gina marayu, abin da al'ummar Amirka ke dauka a matsayin Kaskanci garesu. Wata marubuciya a jaridar Washintog Post mai suna Suzan Phildaz, ta rubuta cewa: 'Da yawa daga kananan yaran da ke da majibinta wadanda ke raye a karkashin iyalan da ke taimakonsu, suna fuskantar duka, wulakanci da mummunan mu'amala, kai! awasu lokuta ma ana kashe su.' Har ilayau Phildaz nacewa: 'Nau'in mu'amalar kowace al'umma tare da 'ya'yanta wata muhimmiyar alama ce da ke nuna hakikanin wannan al'umma.' Har ila yau ta kara da cewa: Adadin kananan yara da ke watse sai kara yawa yake yi a Amirka kullum, har ta kai ga a wasu lokuta `yan sanda na gano jarirai a wuraren tara juji. A irin wannan hali taimakon uwaye mata na kudade ba ya wadatarwa, maimakon haka, babu makawa a samar da wasu cibiyoyi don amsa manyan bukatun wadannan kananan yara."



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next