Gudummawar Mace



Gudummawar Mace Wajan Ginin Al'umma

Mu'assar Al'balagh

GABATARWA

"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan aiki.."Surar Taubati, 9:71.

"Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (dabam-dabam) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..."Surar Hujarati, 49:13.

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da tsarkaka daga lyalansa da zababbu daga Sahabbansa.

Zamantakewar dan Adam ba ta taba zama a wata rana cikin wadatuwa daga mace ba, alhali kuwa ita ke matsayin rabin samuwarsa ko ma fiye da haka. Duk wanda ya nutsa cikin zurfin tarihin dan Adam, zai ga cewa, hatta a lokutan da suka fi koyaushe ci baya, mace na da wata babbar gudummawa, duk kuwa da cewa wannan gudummawa ta faku daga gannai.

Idan har wayewar zamani ta fuskanci yin ta'akidi a kan gudummawar mace (a rayuwa) da ta da yekuwar kiyaye hakkokinta, duk da cewa na bayyane ne kawai, to Musulunci tun farkon bayyanarsa, ya yi kira kan cewa mace ta taka rawarta a rayuwa, kuma ta dauki nauyin da ya hau kanta wajen ginin wayewar bil-Adama. Allah Madaukaki Ya ce:­

"Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): `Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinsu, namiji ne ko mace', sashinku daga sashi yake..." Surar AIi-Imrana, 3:165. Idan har mace a lokacin jahiliyya ta kasance wani kashi da aka yi watsi da shi wanda kuma ya fada karkashin tsiraici da kaskancin matsayi, to a cikin zamantakewar Musulunci ta dawo ta zama mutum wadda ke da abin koyi ga sauran muminai. Tarihin Musulunci ya shaida wasu lokuta masu muhimmanci na wasu fitattun mata, kamar Uwar Muminai

Khadija, da shugabar matan duniya Fadimatu (a.s.).



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next