Imamanci Da Nassi2Suka ce: E. Sai ya ce: Waye ya fi kusanci da Manzo? Suka ce: Kai ne. Sai Abdurrahman dan Auf ya katse maganarsa ya ce: Ya Ali! mutane ne suka zabi Usman, kada ka dora wa kanka laifi (ka damu kanka). Sannan sai Abdurrahman ya kalli Abu Dalha Al’ansari[40] ya ce da shi: Ya Aba Dalha da menene Umar ya umarce ka? Sai ya ce: In kashe duk wanda ya saba wa al’umma! Sai Abdurrahaman dan Auf ya ce da imam Ali: Ka yi bai’a tun da haka ne, in ba haka ba sai ka zama wanda bai bi tafarkin musulmi ba! Kuma mu zartar da umarnin da aka umarce mu da shi a kanka!! Sai Ali (A.S) ya ce: “Kun sani ni ne mai wannan hakki ba wani ba, wallahi zan yi hakuri matukar al’amarin musulmi ya tafi daidai zalunci ya zamanto a kaina ne kawai…â€‌[41]. Wannan kuma hadisi jama’a da yawa suka rawaito shi, ba ya cikin raunanansu ko wadanda ake kokwanto. 9- Wani ya taba cewa da imam Ali ya dan Abi Dalib kai ka kasance mai kwadayin wanna shugabanci, sai ya ce: Ku ne kuka fi ni kwadayinsa kuma ku ne mafi nisa, amma ni na fi kusanci, kuma ina neman hakkina ne, ku kuma kuna hana ni, kuna juyar da fuskata daga gareshi, yayin da ya kafa masa hujja a cikin mutane sai ya juya yana dimuwa bai san me zai amsa baâ€‌[42].
|