Imamanci Da Nassi2



Ya ce: A wata ruwaya sai mutum sha biyu su yi mulki, shida daga â€کya’yan Hasan, biyar daga â€کya’yan Husain, wani kuma daga waninsu, sannan sai ya mutu sai zamani ya lalace. Ibn Hajar ya yi ta’aliki a kan wannan hadisi ya ce: Wannan ruwaya tana da rauni kwarai ba za a iya dogara da ita ba[107].

Wasu mutane suka ce: Zai iya yiwuwa Manzo (S.A.W) yana bayar da labarin abubuwan mamaki da zasu faru da fitinu har mutane a lokaci guda su rarrabu da sarakuna goma sha biyu, da yana nufin wanin hakan da ya ce goma sha biyu da zasu yi kaza da kaza, saboda haka ba komai yake nufi ba sai su zama a lokaci daya…â€‌[108].

Suka ce: Ya taba faruwa a karni na biyar a Andulus kawai akwai sarakuna shida kowanne yana cewa shi ne sarki, akwai kuma na Misira da na Abbasiyya a Bagdad banda wanda yake da’awar shugabanci a duniyar musulmi na daga Alwiyyawa da Hawarijawa[109].

Ibn Hajar ya ce: “Wannan zance ne na wanda bai san wata hanya da wannan hadisi ya zo ba in banda ruwayar da ta zo daga cikin littafin Sahihul Buhari kawaiâ€‌[110].

Samuwarsu a lokaci guda tana samar da rarraba ne, ba zai yiwu ya zama shi ne abin da ake nufi ba[111]. Haka nan ba su yi ittifaki ba a kan wani ra’ayi da ya zo na daga bayanan da suka gabata, sai dai sun yi kokarin rufe ido da kawar da kai daga ruwayar da ta zo daga Annabi (S.A.W) da sunayensu domin ta saba da siyasar Hukuma da Dauloli a Koyarwar halifanci a tsawon zamani, Malaman hadisai sun fitar da wannan ruwayoyi a littattafansu da sanadinsu zuwa ga manyan sahabbai daga manzon Allah (S.A.W)[112].

Abin Da Ya Zo Game Da Nau’i Na Uku

Daga Abi Abdullahi Sadik (A.S) ya ce: Jibril ya sauka wajan Muhammad (S.A.W) sai ya ce: Ya Muhammad! Allah yana yi maka albishir da abin haihuwa da za a haifa daga Fadima (A.S) wanda al’ummarka zata kashe shi bayanka, sai ya ce: Ya Jibril! Aminci ya tabbata ga Ubangijina ba bukata gareni ga abin haihuwa da al’umma ta zata kashe shi bayana, sai Jibril ya hau ya sauka, sannan sai ya sake fada masa hakan. Sai ya ce: Ya Jibril! Aminci ya tabbta ga ubangijina ba ni da bukata ga irin wannan abin haihuwa da al’ummata zata kashe shi. Sai Jibrilu ya hau ya sake sauka ya ce: Ya Muhammad Ubangijinka yana gaishe da kai yana kuma yi maka albishir da cewa zai sanya imamanci da shugabanci da wasiyya a cikin zuriyarsa, sai ya ce: Na yarda. Sannan sai ya aika wa Fadima (A.S) cewa Allah yana yi mini albishir da da da za a haifa daga gareki, da al’ummata zata kashe shi bayana, sai ta aika masa da cewa babu bukata gareni ga wannan da da al’ummarka zata kashe shi bayanka, sai ya aika mata da cewa, Allah ya sanya imamanci da shugabanci da wasiyya a cikin zuriyarsa, sai ta aika zuwa gareshi da cewa na yarda “Babarsa ta dauki cikinsa tilas ta haife shi tilas kuma cikinsa da yaye shi wata talatin ne har sai da ya isa karfinsa ya kai shekara arba’in sai ya ce: Ka sanya mini in gode wa ni’imarka da ka yi mini da ni da iyayena, kuma in aikata aiki na gari da zaka yarda da shi, kuma ka gyara mini a cikin zuriyataâ€‌[113]. Ba domin ya ce ka gyara mini a cikin zuriyata ba, da dukkan zuriyarsa sun zama imamai[114]. Shi’a suna imani da cewa kowane imami ya yi wasiyya da imamin da zai zo bayansa[115].

Sunayen Imamai Sha BiyuA Ruwayar Ahlussuna

1- Jawini[116] ya rawaito daga Abdullahi dan Abbas ya ce: manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ni ne shugaban annabawa Ali dan Abi Dalib shugaban wasiyyai, kuma wasiyyaina goma sha biyu ne a bayana, na farkonsu shi ne Ali dan Abi Dalib na karshensu Mahadi (A.S)â€‌.

2- Daga dan Abbas ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Halifofina kuma wasiyyaina kuma hujjojin Allah bayana goma sha biyu ne na farkonsu dan’uwana na karshensu danaâ€‌. Sai aka ce ya manzon Allah wanene dan’uwanka? Sai ya ce: Ali dan Abi Dalib, Aka ce wanene danka? Ya ce: Mahadi wanda zai cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci, na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya mai albishir da gargadi, da ya kasance bai rage ba daga duniya sai rana daya da Allah ya tsawaita ranar har sai dana Mahadi ya bayyana sai Ruhul-Lahi Isa dan Maryam ya sauka, sai ya yi salla bayansa kuma kasa zata haskaka da hasken Ubangijinta kuma ikonsa zai kai gabas da yammaâ€‌.

3- Jawini da sanadinsa ya ce: Na ji manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Ni da Ali da Hasan da Husain da tara daga â€کya’yan Husain tsarkaka ne ma’asumaiâ€‌[117].


 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next