Imamanci Da Nassi2



1- Ya tara sahabban manzon Allah lokacin halifancinsa sannan ya yi musu huduba yana mai hada su da Allah cewa waye ya ji Manzo (S.A.W) a Gadir khum yana cewa; “Duk wanda nake shugabansa Ali shugabansa neâ€‌, sai ya tashi ya shaida[22].

2- Ali shi ne ya yada wannan hadisin da ya bujuro da shi ga Abubakar da Umar da Annabi yake cewa akwai wanda a cikinku zai yi yaki a kan tawilin Kur’ani kamar yadda na yi yaki a kan saukarsa wanda Abubakar ya yi burin a ce shi ne, haka ma Umar, amma Manzo ya amsa musu da: cewa ba su ba ne. Sannan daga baya Manzo ya gaya wa mutane cewa Ali ne[23].

Wannan ruwaya duk da waninsa sun rawaito ta amma ruwayarsa tana da wani hususiyya domin ya yi ta ne a huduba a gaban mutane, ba hadisi ba ne da ya gaya wa mutum daya ko wasu jama’a, wannan kuwa yana karfafa karfin hadisi game da hakkinsa da yake da yakini da shi, kuma yake da yakini da cewa sauran sahabbai suna da yakini da hakan ba su manta ba.

3- Kuma ya ambaci da yawa daga wadannan hadisai da suke nuna hakkinsa a ranar shura ko bayanta, sai dai an yi sabani kan dalla-dallar maganar da isnadinsa, duk da a dunkule sun tabbatar da hakkinsa, mafi karancin abin da ya hada su da Allah a kansa shi ne abin da Ibn Abdulbar ya fitar a littafinsa yana mai cewa: Ali ya fada wa wadanda suke cikin shura tare: “Ina hada ku da Allah shin akwai wanda Manzo (S.A.W) ya hada shi â€کyan’uwantaka da shi tsakaninsa da shi yayin da ya sanya â€کyan’uwantaka tsakanin musulmi in ba ni ba?

A bayan wannan hadisi Ibn Abdulbar ya sake rawaito wani daga Ali yana mai cewa: Imam Ali (A.S) ya kasance yana cewa: “Ni bawan Allah ne kuma dan’uwan manzonsa, ba mai fadin haka a bayana sai makaryaciâ€‌[24].

An rawaito ta a littafin Kanzul Ummal a wani hadisi mai tsawo daga Abu Dufail ya ce: Ali (A.S) ranar shura yana fadin wannan hadisi…[25].

Wanda abin da shi Ibn Abdulbar ya fitar wani yanki ne daga gareshi, sai dai sanadin Kaznul ummal a kwai jahala[26] a cikinsa, shi ya sa ma aka samu jayayya game da shi, an ce Zafir ya rawaito shi wanda shi mutum ne da ba a san shi ba, wasu kuma sun yi musun sa saboda mataninsa amma ba a la’akari da wannan saboda ya ginu ne a kan fahimta ta cewa an yi bai’a ga Abubakar a kan cewa ijma’i ce ko kusa da hakan wacce ba ta da asasi.

Amma isnadi ya kasance saboda Zafir ne kamar yadda Ibn Abdulbar ya rawaito shi a littafin Isti’ab,[27] Ibn Hajar Askalani ya ce: Zafir ba a tuhumar sa da karya, kuma idan aka same shi a hadisi to hadisinsa yana da kyau[28].

A farkon wannan hadisin, Abu Dufail yana cewa: Na kasance a bakin kofa ranar shura sai aka daga sauti sama, sai na ji Ali (A.S) yana cewa: “Mutane sun yi bai’a ga Abubakar amma na rantse da Allah ni na fi shi cancanta, amma sai na ji na bi domin tsoron kada su koma kafirai wasu suna saran wasu da takobi, sannan sai Umar ya biyo bayansa alhalin na fi shi cancanta kan wannan al’amri, amma sai na ji na bi tsoron kada mutane su koma kafirai wasu suna saran wasu, sannan sai ga ku kuna son ku yi bai’a ga Usman! Ba komai zan ji in biâ€‌, Sannan sai ya ambaci al’amrin shura ya fara bayyana musu falalarsa da fifikonsa da darajojinsa da ya fi su da ita, daya daga cikinsu ita ce wannan bangaren da shi Ibn Abdulbar ya rawaito game da â€کyan’uwantakarsa da Manzo (S.A.W)[29]. Wannan hadisi yana da wani mai karfafarsa da zai zo nan gaba.

4- Daga abin da yake nuna cancantarsa fiye da Abubakar musamman yayin da ya fadi karbar surar bara’a daga Abubakar! Nisa’i ya rawaito da sanadi sahihi daga Ali (A.S) cewa manzon Allah (S.A.W) ya aika shi da bara’a zuwa ga mutanen Makka tare da Abubakar, sannan sai ya sa Ali ya bi shi ya ce da shi: “Ka karbi littafin ka tafi zuwa Makka ya ce: Sai ya cim masa a hanya, sai Abubakar ya koma Madina yana mai bakin ciki, sai ya ce: An saukar da wani abu game da ni ne? Sai Manzo ya ce: A’a, sai dai ni an umarce ni da in isar da wannan ko ni ko wani mutum daga gidanaâ€‌[30].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next