Imamanci Da Nassi2
Wannan mataki na imam Ali (A.S) bayadda za a fassara shi da ma’anar yafi cancanta da ma’anar wanima yana iya rikon jagoranci, wannan afili yake cewa ya yi daidai da ma’ana ceta cancantar kebantaka da shi. Hakanan fadinsa (A.S): “Ko kumain yi hakuri cikin makahon duhu…â€‌. Ma’anarsa abin da ya faru ba kawai kwacen mulki ba ne, sai daiwannan yana zama farkon faruwar canji ne da zai iya kai al’umma gabata, Shi ya sa ya karfafa wa mutane bayan kashe Usman dan Affan yayin da suka zo domin yi masa bai’a: “Ku rabu da ni ku nemi wanina domin tafarki ya bice hujja kuma an yi musun taâ€‌[68], da fadinsa garesu: “Ni inaji muku tsoro ne ku kasance cikin wani yanayi na lokaci, alhalin dacan wadansu al’amura sunfaru sun wuce da kuka karkata zuwa garesu karkatar da kuka zamo ba abin yabo ba ne ku a gunaâ€‌[69].
Dalilan Tarihi A kan Ingancin Mahangar Nassi
Dalilan tarihi a rayuwar Annabi (S.A.W) da Ali a kan cewa Manzo (S.A.W) ya kasance yana yana shiryar da Ali da tarbiyya na daukar sako bayan wucewarsa, yana ba shi ilimi da tunani yana kuma kebewa da shi kowane dare da rana, yana wayar da shi a kan abin da sakon musulunci yake dauke da shi da matsalolin tafarkin har zuwa ranar karshe ta rayuwarsa.
Nisa’i[70] ya rawaito da sanadinsa zuwa ga Abi Ishak, ya ce: An tambayi Kusum dan Abbas cewa, yaya Ali ya zama mai gadon Annabi (S.A.W) banda ku? Sai ya ce: Domin shi ne na farkon haduwa da shi kuma mafi damfaruwa da shiâ€‌.
Haka nan ya rawaito[71] daga Ali (A.S) ya ce: “Na kasance idan na tambaya sai a ba ni, idan na yi shiru sai a fara –gaya- miniâ€‌.
Abu Na’im ya rawaito a littafin Hilyatul auliya daga dan Abbas ya ce: “Mun kasance muna magana a lokacin Annabi (S.A.W) cewa ya ba wa Ali wasiyya (ilimi) saba’in da bai ba wani shi baâ€‌[72].
Nisa’i ya rawaito daga Ali (A.S) ya ce: “Ina da wani matsayi gun manzon Allah (S.A.W) da babu wani mahaluki da yake da shi, na kasance ina zo masa kowane karshen dare sai in ce: Assalamu alaika ya nabiyyallah, idan ya yi gyaran murya sai in koma zuwa ga Ahlina, in ba haka ba sai in shiga wajansaâ€‌[73].
Daga gareshi ya ce: “Ina da shiga guda biyu wajan manzon Allah, daya da dare, daya da ranaâ€‌[74].
Wannan irin tarbiyyantarwa ga Ali da Manzo (S.A.W) ya yi masa ya yi tasirin da Ali ya zama shi ne madogarar kowa makoma ga warware duk wata matsala da aka kasa warware ta hatta da masu jagoranci a wannan lokaci, amma ba a taba samun wata matsala guda daya ba a tarihin imam Ali da ya koma zuwa ga wani mutum ko daya, yayin da a tarihi akwai mas’aloli da dama da dukkkan halifofi suka koma zuwa gareshi duk da kokarin boye wannan matsayi nasa da aka yi.
Amma tarihi ya riga ya tabbatar mana shelantawar da Annabi (S.A.W) ya yi game da hikimar da yake da ita wajan ba wa Ali tarbiyya da ilimi na musamman wanda suna da yawa da suka faru a lokuta daban-daban, kamar hadisuddar, da hadisin sakalaini, hadisin manzila, da hadisin Gadir, da gomomin hadisai[75].
Dalilin Tabbatar Wasiyya Daga Ruwayoyi
Idan nazarin samuwar nassi ya tabbata ita ce kawai hanyar shari’a da Annabi (S.A.W) ya tabbatar da ita a rayuwarsa a tarihi. Kuma imam Ali (A.S) ya ki dukkan wani abu da zai zama makoma ga jagoranci bayan Manzo in ba wasiyya ba, sai ya rage mana mu yi bincike game da dalili ta fuskacin shari’a da yake tabbatar da cewa Manzo (S.A.W) ya yi wasiyya da imam Ali (A.S) da halifanci bayansa, kamar yadda shi ma ya yi wasiyya da halifanci da imamai bayansa.
|