Imamanci Da Nassi2



Shi’a suna da akidar cewa imamancin imam Ali da â€کya’yansa Hasan da Husain da kuma tara daga zuriyar Husain (A.S) duk an samu nassi da ya zo game da hakan daga manzon Allah (S.A.W) wanda kuma kowanne daga cikinsu ya yi wasiyya da mai bi masa, nassosin hadisan sun kasu gida uku ne:

Nau’i na farko: Abin da yake wajabta komawa zuwa ga Ahlul Bait (A.S) ba tare ya fadi sunayensu ba; kamar hadisin sakalaini da hadisin safina wadanda mutawatirai ne daga Shi’a da Sunna.

Nau’i na biu: Abin da yake iyakance adadin halifofin Annabi da cewa sha biyu ne kuma daga kuraishawa daga Bani Hashim suke, Wannan kuwa adadi ba ya dabbakuwa sai a kan imamai na Ahlul Baiti (A.S), sabanin idan an dabbaka shi a kan wasunsu.

Nau’i na uku; Hadisan da suka zo da ambaton sunayensu (A.S) har guda goma sha biyu, ta hanyar Shi’a da Sunna.

Amma Abin da Ya Zo A Nau’i Na Farko

Tirmizi ya rawaito daga Jabir yana cewa: “Na ga manzon Allah (S.A.W) a hajjin bankwana yana kan taguwarsa da shi da Ali (A.S) sai na ji shi ya ce: “Ya ku mutane na bar muku abin da idan kun yi riko da su ba zaku taba bata ba, littafin Allah da Ahlin gidanaâ€‌[76]. Tirmizi ya ce: A wannan babi kawai an karbo wannan hadisi daga Abi Sa’id da Zaidu dan Arkam da Huzaifa dan Asid.

A Sahih Muslim da Masnad Ahmad dan Hanbal da Sunan Darimi da Baihaki da wasunsu kuma lafazi ga na farko yake daga Zaid dan Arkam ya ce: “Manzon Allah ya tsaya yana mai huduba a wani ruwa da ake kira Khum da yake tsakanin Makka da Madina…

Sannan ya ce: “Ya ku mutune ku sani ni mutum ne da dan sakon ubangijina ya kusa zuwa sai in amsa masa, na bar muku nauyaya biyu; Na farko littafin Allah da akwai shiriya a cikinsa, ku yi riko da littafin Allah da kuma Ahlin gidanaâ€‌[77].

A cikin sunan Tirmizi da masnad Ahmad da lafazin Tirmizi: “Na bar muku abin da da idan kuka yi riko da shi ba zaku taba bata ba bayana, daya ya fi daya girma: littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa, da kuma Ahlin gidana, ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki, ku duba ku gani yaya zaku maye mini a cikinsuâ€‌[78].

Daga irin hadisai da suka zo akwai hadisin safina, Manzo (S.A.W) yana cewa: “Ku sani misalin Ahlin gidana a cikinku kamar jirgin Nuhu ne, wanda ya hau ya tsira wanda kuma ya bar shi ya nutseâ€‌[79].

Wasu malamai da dama suna ganin Ahlin gidan Annabi (S.A.W) su ne mutum biyar masu girma da daraja da ya hada da annabin kansa (S.A.W) da kuma Ali da sayyida zahara da Hasan da Husain (A.S).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next