Imamanci Da Nassi2Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice
Allah bai halicci mutum domin wasa ba kawai, ya halicci mutum domin ibada da shiriya ne; Annabta tana dauke da nauyi ne na gargadi da isar da sakon Allah, imamanci kuma yana dauke da shiryar da mutane zuwa ga wannan shiriya da kuma kama hannun mutane domin su bi wannan shiriya da annabawa suka zo da ita a aikace, ba zai yiwu a san annabta ba sai da wahayi da mu’ujiza, kuma ba zai yiwu a san imamanci ba sai da nassi da yake nuna ma’sumi. Bai’a ga shugaba ma’abocin wilaya ta gaskiya ba ita ce take tabbatar da wajabcin binsa[118] a matsayinsa na imami da Annabi ya yi wasiyya da shi da binsa ba, kamar yadda ba ta iya tabbatar da imamanci da halifancinsa[119]. Amma shura ba ta iya zama maimakon wasiyya kamar yadda hukuncin da shura take zartarwa ba ya zama wajibi a kan imami ya yi aiki da shi. Manzo (S.A.W) ya yi aiki domin karfafa nassi da wasiyya a kwakwalen musulmi ne, sannan tarihi bai taba tabbatar da zuwan wani abu daga gareshi ba sai wasiyya da nassi da suka zo a cikin hadisai. Amma imam Ali aikinsa gaba daya ya tsayu a kan nazarin nassi sa waiyya ne da zuka zo a cikin hadisai yayin da zamu ga yana musun duk wani abu da ya sabawa hakan. Daga karshe mun samu dalili na ruwayoyi daga Shi’a da Sunna da suke tabbatar da halifanci da imamanci ga imamai goma sha biyu da nassin hadisin Annabi (S.A.W) wanda na farkonsu yake shi ne Ali dan Abi Dalib, na karshensu Mahadi (A.S) da wannan ne wannan nazari da mahanga zata zama ita kadai ce hanyar shari’a da take tabbatar da hanyar ibada da shiriya. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai
Littattafan Da Mafassarin Littafin Ya Wallafa:
1. Hakkoki a musulunci 2. Raddin sukan auren mace fiye da daya 3. Mace a al’adu da musulunci 4. Tarbiyyar yara a musulunci
|