Tarbiyyar Yara A Musulunci



Gasa Tsakanin Yara

Ana iya shiryawa yara gasa kamar ta tarihin Annabawa da ta karatun Kur’ani da ta iya salla a aikace da alwala, ko kuma a ce duk wanda a wannan satin ba a ji ya yi zagi ba to babansa zai kai shi Gidan zuu ya yi kallon dabbobi kuma ya saya mishi askiran a can Gidan zuu din mai dadi, kuma a sani duk wanda ya kiyaye wajibi ne a yi masa abin da aka alkawarta da gaggawa idan ba haka ba zai zama abu mafi sauki wajan rusa tarbiyya da himmar yaro.

Haka nan ma idan an yi alkawari za a sayo masa alewa mai dadi ya kamata ta zama an saya, amma a kyautar gasa sai a saya da yawa, wanda ya yi na daya sai a bashi kaso mafi girma haka nan na biyu yana binsa har zuwa na karshe, domin yara ba kamar manya ba ne idan ba a basu ba, to a karya zuciyarsu ko da kuwa ba su yi nasara ba a gasar, gasa tana daga cikin mafi muhimmancin hanyar tarbiyyatar da yaro. Duba mana ‘yan’uwan Yusuf (A.S) a yayin da suke cewa: “Suka ce: Ya babanmu lallai mu mun tafi muna gasar tsere kuma muka bar Yusuf a wurin kayanmu…”[13]. Sa’annan wannan yana nuna mana muhimmancin wasanni da tsalle-tsalle ga yara da samari.

Karbar Uzurin Yara

Idan yaro ya yi laifi kafin a yi masa fada ko bayan an yi masa din sai ya bayar da uzuri ko ya nuna ya tuba in za a doke shi ko ana yi masa fada aka ga ya ji tsoro to a nan kada a ki karbar uzurinsa, domin kamar yadda muka san babba yana bayar da uzuri a karba haka yaro, muna iya cewa nasa ya fi na babba muhimmanci ba kadan ba.

Yana da muni kwarai idan ya bayar da uzuri ko ya ji tsoro ya tuba a ki karba ko a gwale shi, wannan yana daga hanyar rushe tarbiyyarsa, yana da kyau iyaye mu sani cewa yaro abu ne mai santsi sosai da laudi, kuma ya kamata mu sani cewa kamar yadda muke son Allah ko wasu su karbi tubanmu da uzirinmu, mu ma yana kanmu ne mu karba daga garesu, saboda haka tsanantawa game da al’amarin yaro yana karya shi ne yana kuma lalata masa tarbiyya ne.

Canza Waje Ga Yara

Idan kana unguwa da ka san yaronka lallai zai iya lalacewa to yana kanka ka dauki mataki kwakkwara a kai koda kuwa zai kai ga raba shi da wurin ko kai ka bar wurin gaba daya, kamar ka ga yaro ba shi da wasu abokai a unguwar sai na banza kuma ba zaka iya raba shi da su ba kuma babu wata hanyar gyara sai dai ka bar wurin ko kuma shi a sauya masa waje ko garin da aka san zai gyaru ya tashi salihin mutum to duk wannan yana kan iyaye su yi kokari a kan haka.

Duba ka ga Annabi Yusuf (A.S) da zai rasu ya yi wa ‘yan’uwsa nasiha da su bar kasar Masar suka ki, sai bayan kusan shekara dari bakwai zuwa dari tara kamar yadda yake a tarihi sun sha wahala a hannun fir’aunoni na Masar sannan Annabi Musa (A.S) ya samu damar fitar da su daga wannan kangi na wahala. Haka ma Manzo (S.A.W) ya bar Makka zuwa Madina don ya gina al’umma ta gari mai karfi da umarnin Allah (S.W.T) kuma gabanin haka ya umarci sahabbansa (R.A) da su yi hijira zuwa Habasha.

A hirar da gidan talabijin na IRNA channel na shida ya yi da Shaikh Asifi a ranar asabar 16 August 2003 shehin ya nema daga mutunen Iraki da su bar kasashen turai su koma gida saboda gudun lalacewar tarbiyyar ‘ya’ya da canjawar al’adu da tarbiyya, kuma ya kara da cewa a kwanan nan wani daga irakawan ya yi masa waya yana gaya masa amsar da wata shugaban makarantar sakandare a daya daga kasashen turai ta ba shi lokacin da ya je neman kada a sanya ‘yarsa a cikin darasin rawa da kide-kide na makarantar, sai shugaban makarantar ta cire tubaranta ta kalle shi daga sama har kasa sannan ta ce da shi: Ku sani idan kun iya kare ‘ya’yanku ko kun ci nasarar tarbiyyatar da su ba zaku iya kare jikokinku ba daga daukar al’adunmu kuma kuna ji kuna gani ba yadda zaku yi.

Saba wa Yara Da Wata Al’ada

Kada iyaye su sabawa yaro da wata al’ada kamar kodayaushe duk abin da ya tambaya dole ne ya samu, irin wadannan yara duk ranar da aka hana su ko babu to wannan yana nufin su tayar da fitina da rigima. Haka ma suna iya daukar na wani wata rana domin ba su san su nema su rasa ba, ya kamata a wasu lokutan a saba wa yaro da cewa in Allah ya yarda zai kawo mana na baka in an jima, har ya saba da sauraron warwarar matsalarsa, amma ya danganta da shekarun wadanda suka san babu ne.

Haka ma bai dace ba a saba masa da abin da manya ya kamata su sani kamar kudi, ya kamata ne a saba wa yaro da ba shi abin da zai ci a makaranta kamar biskit da sauransu ba a saba da ba shi kudi ba yana kashewa, irin wadannan yara in ba a lura ba ranar da ba a ba su ba suna iya dauka ko da iyayensu ba su sani ba. Ba a son idanun yaro su san kudi sosai in ba ya haura kananan shekaru ba, amma wannan ba zai iya hana aikensa ba amma ya zama an rubuta masa takarda ne da aka nade kudin a ciki.

Kiyaye irin wadannan abubuwa yakan iya sanya yaro ya saba da dangana idan babu, hakan yakan sanya shi ya nisanci rashin godiya ga iyayen da ganin sun takaita masa wajan kyautatawa, domin idan sun nuna masa su ma suna jira ne zuwa wani lokaci Allah ya buda musu su ma su ba shi, wannan zai taimaka ya san Allah ne yake bayarwa, sannan zai san iyayensa su ma suna nema daga Allah ne, kuma zai koyi tawakkali da dangana da abin da ya samu, da rage masa kwadayi, ko rashin yarda da hukuncin Allah, haka nan zai kara masa sanin cewa akwai Allah  kuma shi ne mai bayarwa mai hanawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next