Tarbiyyar Yara A Musulunci



c. Sanar da shi yadda zai fuskanci matsalolin da suka addabi al’ummar musulmi, da kuma sanya masa cewa yana da karfin da zai iya kawo karshensu.

d. Yi masa bayanin dalilan da suka sanya al’ummar musulmi ta samu ci baya da dulmiya cikin jahilci da mummunan halin da ta fada ciki, da kuma nuna masa shi zai iya kaucewa wannan kuma zai iya maganinsa.

e. Yi masa bayanin yiwuwar gyara da za a iya samarwa ta hanyar amfani da karfin da al’ummarsa take da shi.

f. Yi masa bayanin mummunan halin lalacewar kyawawan halaye da na zamantakewar al’umma da al’ummar da take da’awar ci gaba ta fada cikinsa, da sauran matsaloli da suke fama da su.

6- Sanya lura da karfafawa a kan babbar gudummuwar da telebishan, da radiyo, da mujallu, da kissoshi masu hoto, da labaru zasu iya bayarwa wajan tarbiyyar yara da gina su[19].

Don haka ne nake nasiha ga mutane da su yi duba zuwa ga Gidan Abrar wato Gidan Sayyidi Ali (A.S) da Fadima (A.S) da ‘Ya’yansu Hasan da Husaini (A.S) a kuma a karanta kissarsu da ta zo a cikin surar Insani, da alwashin da suka yi na azumi, da kuma sadakar da suka yi da abincinsu a kwana uku: ga maraya, da miskini, da kuma ga ribataccen yaki[20], domin karanta irin wannan kissoshi zai sanya mana daukar ilimi da darussa masu yawa game da yadda ya kamata salihin gida mai tarbiyya ya kasance.

Godiya ta tabbata ga ubangijin talikai

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:

Kur’ani mai girma

Tsari da kayyade iyali Na mawallafin

Yeksado fanjo mauzu’ az kur’ane karim, Akbar Dehkani



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next