Tarbiyyar Yara A Musulunci



Lokacin Annashuwa

  Yana da muhimmanci samar wa yaro lokaci na annashuwa da shaye-shaye da tande-tande, da shakatawa da filin wasanni, abin haushi a kasashenmu rashin ko in kula na masu tafiyar da kasar da halin talaka da na yara ya munana kwarai da gaske, ta yadda kana iya samun nahiya ko yanki ko unguwa da tana da mutane sama da miliyan amma ba su da filin wasa da na shakatawa da na wasannin yara ko daya sakamakon maciya amanar al’umma da suka yawaita da ba sa jin zafin halin da talaka ko kananan yara suke ciki, kuma babu ruwansu ko kadan da lafiyarsu ko annashuwarsu, don haka yana kan iyayen yara su nemi hakkin haka wajan hukuma don walwalar ‘ya’yansu.

   Da farko akwai irin wadannan filayen da dama, amma yanzu mayun filaye sun kame kurwar irin wadannan filaye da hadin bakin maciya amanar mutanen unguwa na karamar hukuma ko jaha, su kuma mutanen unguwa ba su kula da bin hakkin ‘ya’yansu ba, wani abin takaici babu wannan a tunaninsu, wani lokaci ba su ma san hakkin nasu ba.

Wasi Nasihohi Da Hanyar Tarbiyyar Yara

Daga cikin irin nasihohi da wasu littattafai suke tattare da su game da tarbiyyar ‘ya’ya, musamman idan mun yi la’akari da cewa yaro yana daidai da farar takarda ce wacce duk wata tarbiyya da aka ba shi ita ce takan yi masa tasiri a rayuwarsa. Kuma yaro yana dauke da yiwuwar ya zama kamilin mutum wanda kyakkyawar tarbiyya ce zata iya daidaita shi, ko kuma ya samu mummunar tarbiyya ta rushe wannan karfin zama salihi na gari da yake kunshe da shi. Daga cikin irin wadannan matakai kuma hanyoyi masu muhimmanci akwai:

1- Dasa wa yaro jin nutsuwar zuci da rai, da kama hannunsa domin daukaka matsayinsa, wannan kuwa yana iya kasancewa ne ta hanyar rashin wulakanta shi, da sanya masa jin daukaka da kamala, ko rashin nuna masa gazawarsa. Don haka abin da ya kamata shi ne: a rika tattaunawa da shi, da neman shawararsa da nuna masa inda ya samu rauni, domin ya taso mutum mai dauke da jin cewa zai iya kasancewa jagora a kowane fage.

2- Rashin kallafa wa yaro abin da ya fi karfinsa, ko kuma ayyukan da ba ya son su, domin gudun kada ya gajiya ya kasa, wannan kuma yana iya janyo masa jin kasawa da rushe himmarsa.

3- Dada wa yaro kaimi domin ya zama wani babban mutum ta hanyar girmama masa manyan mutane da suka gabata ko rayayyu, da yi masa bayanin sirrin abin da ya sanya suka zama manyan mutane masu daraja da kuma hanyoyin da suka bi domin kai wa ga wannan matsayin.

4- Kula da yaro domin kada girman kai da ruduwa da kansa su same shi domin yana ganin ya fi sauran abokansa kokari a karatu, da koya masa siffofin dabi’u kyawawa da ya kamata ya siffantu da su, da nuna masa wadannan ni’imomi da yake da su daga Allah ne kuma shi zai godewa.

5- Yi wa yaro bayanin abin da al’ummarsa take ciki dalla-dalla da kuma yadda zai bayar da tasa gudummuwa domin kawo ci gaban al’ummarsa ta hanyar:

a. Samar masa akida ta gari da zai doru a kanta.

b. Bayanin gudummuwar da al’ummarsa ta bayar wajen ci gaban dan Adam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next