Tarbiyyar Yara A Musulunci



Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne kuma ribataccen yaki, a shekara bakwai kuma dan’uwa ne kuma waziri”[18]. Wannan Hadisi yana nuna mana shekara ishirin da daya da zaka yi tare da yaro da irin mu’amalar da zaka yi da shi a kowace shekara daga shekarun bakwai.

Na uku: Koyar da yaro kada ya cuci wani ta hanyar sanya tausayin al’umma a zuciyarsa kuma da koya masa kada ya karbi a zalunce shi, da tausaya wa wanda aka zalunta da nakasassun mutane kamar mai bara da talaka, wannan yana iya faruwa ta hanyar ba su labarai da tarihi na magabata domin ya yi tasiri a kansu.

Na hudu: Sanar da yaro tarihi da labaran yadda kasarsa take da kuma abin da kakanninsu suke a kai na alheri da kwadaita masa wannan, kamar ba shi labaran Shehu Usman dan Fodio (R.A) da wahalar da suka sha da kuma zuwan turai kuma da sanar da shi kabilun kasarsa da hakkokkinsu a kansa, da koya masa yadda zai kiyaye hakkin sauran abokan zamansa na kasarsa musulminsu da wadanda ba musulmi ba.

Na biyar: Nisantar kalmomin banza da gulmar wasu da cin namansu da duk ma abin da bai dace ba a gaban yaro da ma dukkan wani abu mummuna domin shi ma yana dauka kuma ya aikata, wato abubuwan da aka hana na haram bayan haramcinsu yin su a gaban yaro yana dada munana su domin yana nufin bata asasin ginin al’umma wato yaro.

Na shida: Yi wa ‘yayanka addu’a kullum da alheri na Duniya da na Lahira, wannan ya zama abin da ba zaka taba mantawa da shi ba, koda kuwa ka manta da yi wa kanka addu’oi to kuskure ne babba ka manta da yi wa yaranka.

Na bakwai da takwas: Shawartar yaro kan wasu abubuwa kamar ka ce da shi me za a dafa a gida a yau, ko kuma ranar juma’a idan mun dawo daga masallaci da yamma a ‘yan’uwanmu su wa zamu ziyarta? ko kuma ina zamu yawon shakatawa a wannan watan.

Har na tuna wata rana da Ramadan wani daga dalibanmu na bangaren Hausa da suke karatun Hausa a Jami’ar Azad da take a birnin Tehran ya gayyace mu gidansa shan ruwa sai na ji yana sharwartar ‘yarsa wane film ne ya kamata ya sanya mana? Ita kuwa sai ta mayar wa Uban da cewa: zabi yana hannunmu duk wanda muke so. Kafin nan shi da dansa da suka zo daukarmu a mota sai yakan ce da shi dan da yake tuka mu cewa: Ai wannan abokina ne kuma dana.

Haka nan yana da muhimmanci mai girma a rika gode wa yaro duk sa’adda ya yi wani abu na kirki da yabonsa kan haka don a kara masa himma a kan abubuwan da yake yi na alheri.

Na tara: Nuna masa kuskure kan abin da ya yi na kuskure da nuna masa cewa zai iya kai wa ga wani abu da zai cuce shi a Duniya ko a Lahira ko a duka gida biyu.

Na goma: Hanyar kwadaitawa ta fi yawa a kan hanyar tsoratawa, wato a fi gaya masa Allah zai ba shi kaza a Lahira in yana biyayya ga iyaye ko wani aiki na alheri maimakon a rika cewa: Ai in ka mutu ma binne ka a kasa kuma kunama da maciji da mala’ika mai sanda ta wuta su zo su kama ka su cije ka. Irin wannan ya zama kadan ne domin yana iya sanya masa tsoron komai, ko ya kashe ruhinsa, ko ya sa masa kosawa daga jin nasihar, idan ya yi yawa tsoro yana iya kama shi da zai iya hana shi fita ko waje ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next