Tarbiyyar Yara A Musulunci



Don haka yana kan iyaye su saya wa yaro abin da zai rika debe masa kewa. An ce an yi wani mutum da ya hana yaransa wasa ko kadan sai yaron ya taso dolo ba kuma abin da yake so sai wasa irin na yara, da ya kai shi wajan malamai masana halin dan Adam sai suka gano ba a bar shi ya yi wasa ba ne yana yaro saboda haka suka umarci uban da ya sayo masa kayan wasa. Haka nan ya yi ta wasa har wata rana da kansa ya bar kayan wasan, da iyaye suka ce ga kayan wasanka can sai ya ce: Ai ni ba karamin yaro ba ne, ta haka ne a ka yi maganin matsalarsa.

Kula Da Yara

Bai dace ba ka kawo yara da yawa a Duniya ka watsar da su a kan titi, abin da yake a kan uba shi ne ya kawo wanda zai iya tarbiyyarsa a duniya ko da mutum daya ne. A wannan zamani Allah ya yassare hanyar da tsarin haihuwa ko kayyade iyali[7] cikin sauki, Saboda haka kada ka kawo yara ka watsar a titi domin hakan yana iya cutar da su ya kuma cutar da al’ummarka. Ba yadda za a yi Manzon Allah (S.A.W) ya yi alfahari da zauna gari banza ko barayi da sauran mutanen banza a cikin al’umma, mutanen da Manzon Allah (S.A.W) yake so su yawaita a al’ummarsa su ne salihai da sauran mutane na kirki na gari, da irinsu ne kuma zai yi alfahari.

Saboda haka dole ne ka sani cewa in ka kawo mutum duniya ka tabbatar da ka tarbiyyantar da shi, idan daya zaka iya tarbiyyantarwa sai ka kawo daya idan goma ko dari zaka iya to ya halatta ka kawo su matukar zaka iya tarbiyyatar da su da tanadar musu abin rayuwar yau da kullum, da karatunsu, da ci da shansu da sauransu. Idan ka yi naka kokari sai kuma ka yi addu’a Allah ya yi maka nasa, al’amarin ba kamar yadda wasu suke yi ba ne na ko-in-kula da rashin tashi tsaye sannan kuma sai su ce Allah yana nan, alhali kuwa sun san cewa Allah yana taimakon wanda ya tashi ne.

Su Waye Abokan Yaronka?

Yana da kyau a kula da abokan yaro da zaba masa abokai salihai na gari kamar yadda idan za a yi aure ake zaba masa uwa mumina, a sani bayan iyaye ba wanda ya fi yi wa yaro tasiri irin abokai, don haka da iyayen yara zasu yi kokari su hada ‘ya’yansu abota da yara nagari da abota ta yi kyau, haka nan ma a ba su kissoshi wadanda kan iya taimakawa su nisanci yaran banza.

Duba dan Annabi Nuhu (A.S) ka gani da ya gwammace gwara ya bi abokansa kan dutse da ya bi babansa jirgin ruwa[8], Saboda haka abokai da uwa wani abu ne na farko da su suka fi yin tasiri a kan yaro fiye da kowa. dan Annabi Nuhu babu wani wanda ya yi masa tasiri ya bar babansa sai uwa munafuka kuma da abokai.

Sanin wadanda yaro yake mu’amala da su a waje yana da muhimmanci, saboda haka ne ake son ba wa labarin da yaro yake kawowa muhimmanci domin a san yaya yake tunani shi da abokansa kuma wane irin hali suke da shi, domin ta haka ne za a iya gyara tunaninsu.

   Daga cikin Wasiyyar da Imam Ali (A.S) ya yi wa dansa Imam Hasan (A.S) shi ne: Ya dana!: Ka kusanci ma’abota alheri ka zama daya daga cikinsu, ka nisanci ma’abota sharri ka nisanta daga garesu[9].

Ka zauna da mutane na kirki domin ka zama daga cikinsu, ka nisanci mutanen banza don kar ka tasiranta da su ka zama daga cikinsu.

Zama Tare Da Yara

Wani lokaci iyaye ba sa son yaro ya zauna wajansu ne don su kansu ba su kiyaye abin da ya kamata, sai ka ga ba abin da suke sai gulmar mutane, don haka ne ma sai su ce da yara: Kai! ku tashi suna nan suna jin duk abin da ake cewa. To iyaye su sani wannan ba shi da kyau ko kadan, yaro dan koyi ne abin da yake gani shi zai tashi da shi, Shi ya sa idan kana so ka yi wa yaro fada kan wani abu to ya fara ganin daidai a aikace daga gare ka, misali kana son yi wa yaron fadan zubar da abinci in yana ci, ko ya yi bismillah in zai ci, ko hamdala idan ya kare, ko wanke hannu kafin ci da bayan ci, ko kula da salla da zuwa masallaci, ko idan wani yana magana ya saurara kada shi ya yi magana, ko kada ya yi zagi, to duk irin wannan kafin ya yi masa tasiri yana da bukatar ya gani ne a tare da kai a aikace, idan ba haka ba babu yadda za a yi ya yi masa tasiri.

Misali, idan kina so yaronki ya san yadda ya kamata ya kira sunan babansa, sai ki rika kiran uban da wannan sunan ba kina kiransa da wani suna ba sannan kina son yaron ya rika kiransa da wani sunan daban ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next