Tarbiyyar Yara A Musulunci



Shi ya sa Malaman tarbiyya suke cewa: Yana da wahala ga mutum ya canja da wuri bayan ya yi shekaru arba’in kan wani ra’ayi, misali idan mutum ya kai shekara arba’in ba ya sallar dare to yana da wahala ya iya jurewa ya dage a kai, Shi ya sa idan saurayi ya dore a kan hanya ta gari to yana da wahala ya canja Sai dai idan ya zama akwai wani sirri tsakaninsa da Allah da ba shi da kyau, ko kuma lallai zuciyarsa ba ta kama hanya ta gari ba, ko ba ta doru bisa mahanga sahihiya da Allah ya dora Addininsa a kai ta hannun Manzonsa (S.A.W) ba.

Haka ma idan ya zama yana da dauda a zuciya kamar hassada ko mugun kulli kan bayin Allah na gari to duk wannan yana iya tasiri wajan lalacewarsa koda yana ayyuka ta bangaren ibada a nan ba mamaki ba ne karshensa ya ki kyau. Duba Bil’am dan Ba’ur mana ka gani da malami ne shi amma saboda ya yi wa Musa (A.S) hassada sai ya lalace, haka ma Iblis yana daga mala’iku masu ilimi na koli, amma sai ya yi hassada, shi ke nan sai ya kaskanta, darajarsa ta yi kasa.

Shi ya sa ya zo a wata ruwaya cewa: Kada a duba tsawon ruku’u ko sujadar mutum, ta yiwu wata al’ada ce da ya saba da ita, idan ya bari sai ya ji babu dadi, amma a duba ayyukansa da mu’amalarsa. Kamar wanda ya saba da sallar jam’i ko ta dare ko azumin nafila amma ba sa tasiri a ayyukansa.

Haka ma yaro idan ya saba da wani abu haka zai taso da shi a matsayin saurayi, idan da ya saba da karatu sai ya zama saurayi to ba zai iya bari ba kuma haka zai manyanta, haka kuma zai tsufa matukar wani yanayi na tilas da lalura bai fado ba. Amma yaron da ya taso yana bin ‘yan iska da samarin banza yaya zai taso? Don haka ne tarbiyyar yara take bukatar hukuma, da iyaye, da ‘yanuwa, da makwabta, da malamai, duk su sa hannu wajan tarbiyyantar da ilmantar da yara da samarin al’umma domin a samu al’umma ta gari.

Kur’ani Ya Yi Nuni Da Mu’amala Da Yara

Kur’ani mai girma ya himmantu da tarbiyyar yaro da kula da shi, don haka ne a ayoyi masu yawa ya yi magana game da ‘ya’ya da hakkokinsu, da yadda ya kamata a kalle su, da zama da su, da zamu iya kawo su a dunkule kamar haka:

1- ‘Ya’ya adon rayuwar duniya ne: Kahafi: 46.

2- ‘Ya’ya su ne asasin jarrabawa daga Allah: Tagabun: 15.

3- Wasu daga ‘ya’yanmu makiyanmu ne: Tagabun: 14.

4- Kada ku damu da nauyin ‘ya’yanku a kanku: An’am: 151.

5- Kada ku yi alfahari da yawan ‘ya’yanku: Saba’: 35.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next