Tarbiyyar Yara A Musulunci



Tsawata wa Yara

Yana da kyau idan ka ga yaronka yana yin abin da kasan ba mai kyau ba ne ka nuna masa fushinka a kai da rashin jin dadinka, ya san cewa wannan abin na iya bata maka rai da ba zai iya ganin murmushinka ba, amma a sani yana bambanta daga laifi babba da karami sannan kuma daga yaro zuwa wani yaro daidai gwargwadon bambancin shekarunsu, sannan kuma matakin farko ba shi ne ka fara dukan yaro ba domin ta yiwu shi a wajansa bai san wannan laifi ba ne, da ya sani watakila da bai aikata ba.

Amma idan laifin dan karami ne ko ba shi da tasiri wajan bata tarbiyya a nan ya isa ka yi masa nuni da shi cikin labaru, ko magana, kamar Allah ba ya son haka, da makamancin wannan. Wato abin da yake bukatar tsanani a tsananta wanda yake bukatar sauki a saukaka ba komai tsanani ba ko komai da saukakawa ba wannan kuskure ne babba.

Haka ma wannan yana da bambanci tsakanin shekarun yara da suka bambanta, amma ma’aunai suna iya zama a gane su da hankali, kamar yaro dan shekara daya da rabi ya rika kiran sunan abokanka da sunansu domin ya ji kana kiran su da wannan sunan, a nan ba bukatar ka tsawata ka ce bai da ladabi domin bai ma san me kake nufi ba a nan, amma dan shekara bakwai yana iya gane wannan, akwai misalai masu yawa a kan haka.

Saboda haka a tsawatawa kada a kuskura duka ya zama mataki na farko wannan yana iya saba masa da dukan har ya zama ba ya magani, haka nan ma yana iya kasancewa shi a lokacin bai san wannan abin laifi ba ne. Sannan kada ka ga kai ka haife shi idan ya zama akwai zaluntarsa ko cutar da shi da daukar matakai sabanin na shari’ar Musulunci Allah (S.W.T) zai yi maka hisabin rashin kiyaye amanar da ya ba ka.

Duka Da Tsawa! Ga Yara

Duka yana daga cikin makami da manya kan yi amfani da shi a kan yara, amma ya kamata su sani cewa don ka haifi yaro ba yana nufin kana da ikon cutar da shi ba[10], domin in ka zalunce shi Allah zai yi sakayya a kan haka. Bari ganin ka haife shi wannan amana ce da Allah ya ba ka, shi ya sa uwa, ko malami, ko makwabci, ba su da ikon dukan yaro sai da izinin Shugaban daular Musulunci, ko babansa[11] a wajan wasu malamai. Sayyid Sistani yana cewa: Ya halatta dukan ‘yan makaranta idan suka cutar da wasu, ko suka aikata haram, amma da izinin waliyyansu (uba), kuma dole ne dukan ya kasance ba mai sanya fata ta yi ja ba (ta tashi), idan kuwa ya kai ga hakan sai an biya diyya[12].

Shi ma uba ba kawai ya doki yaro ba, sai dai idan akwai maslaha kuma akwai tsammani mai karfi na cimma wannan maslahar, kuma ya zama ba ya fitar da jini, kuma ba ya lahanta naman jikinsa, ko kashinsa, ko canja masa launin fata, da sauransu. Shi ya sa bai kamata a ajiye bulala domin duka ba sai dai don tsoratarwa ga laifin da aka san haka zai yi tasiri wajan tarbiyyarsa. Misali; bai kamata a ajiye bulala don yaro ya ci abinci ba, yaron da ba ya cin abinci yana bukatar likita ne ba duka ko ajiye bulala ba, domin ta yiwu da bitamin “C” cokali uku matsalarsa ta warware.

Amma wasu iyayen sun dauka komai duka ne maganinsa sai su yi ta dukan yaro ko tsawata masa alhalin da yawa wasu abubuwan malami, ko likita, ko makwabci, ko abokai, su zasu iya warware su ga yaro ba iyaye ba. Wani abin ma laifin iyaye ne amma sai su doki yaro: kamar yaro ya ga suna wani abu shi ma sai ya yi, kamar wani da yake shan taba amma da ya ga yaronsa yana sha a boye sai ya zane shi.

Kausasawa da tsanantawa a kodayaushe ba sa magani ga yaro sabanin tausasawa da nuna kauna da mayar da shi abokin hira, da cin abinci, da zama tare, da tafiya yawo ko unguwa tare da shi, a bisa tarbiyyar da muka samu wajan iyayenmu wannan shi ya fi yi mana tasiri. Yawancin wadanda aka horar ta hanyar kausasawa da takurawa ana bata su ne su taso mutane masu kekashewar zuciya da bushewar zuciya da rashin tausayi da rashin kunya, har ma sukan iya jin ba a kaunarsu ne don haka sai su kama hanyar iskanci da rashin kunya, ko su yi tunanin daukar fansa kan wanda ya azabtar da su, a wani lokaci ko da kuwa uba ne.

Ka taba jin labarin wani dalibi da a furamare da malaminsu ya gallaza masu, bayan ya gama jami’a sai ya zama shi ne mai kula da fayel din Furamare Board a jahar tasu, wata rana yana binciken fayaloli sai ya ga malaman makarantarsu ta furamare, da ya duba sai ya ga sunan malamin wanda a wannan lokaci har ya manta da malamin amma ganin fayel din sai ya tuna masa shi, saboda haka sai ya batar da fayel din, a lokacin da aka zo Pepa red sai ya zama shi malamin ba a ga na shi fayel ba, a sakamakon haka ya rasa nasa albashi da ma aiki, ya zama sai dai ya je wajan abokansa in an dauki albashi don su taimaka masa da wani abu na cefane.

Kamar yadda ya gabata cewa dukan yaro ba shi da kyau in ba wajan tilas ba, haka ma daka wa yaro tsawa ba shi da kyau domin yana iya haifar masa da ciwon tsoro ko ya firgita shi abin da kan iya haifar masa da ciwo a jikinsa ko raunin zuciya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next