Tarbiyyar Yara A Musulunci



Kamar yadda tsoratarwa ba ta da kyau a wajan tarbiyyar yaro haka ma zagi ko duka ba shi da amfani sai dai wani lokaci da ya zama lalura kuma da zato mai karfi na maganin rashin jin nasa, amma zagi koda sau daya ba ya iya zama warwara ko hanyar tarbiyya, a nan yana zama sabanin yadda ake zato ne domin wannan yana zama koya masa zagi ne kenan.

Hanyar Tarbiyyar Yara

Bai kamata ba tarbiyyar yara ta zama an gina ta a bisa tsoro ko fadin karya, ko yaudara, ko tsanantawa, wannan kuskkure ne babba, yana da kyau a dora tarbiyyar bisa sanin Allah da koya masa cewa Allah da yake ko’ina yana ganinka duk abin da kake yi, ko kuma babansa ba zai yi masa kaza ba in yana wani abu maras kyau amma da sharadin zai rika ganin kyautatawa idan yana kiyayewa.

Wata hanya mai amfani shi ne hanyar shagaltar da danka da kayan wasa a gida musamman idan lokaci ne ba na karatu ko bacci ba, da daukarsa wani lokaci zuwa filin yara don ya yin wasanni kamar lilo, da kwallo, da guje guje. Wannan kan iya sanya yaro ya taso da farin ciki da nishadi, sannan ya ji ana sonsa ya rika alfahari da iyayensa da ganin kyautatawarsu gare shi. Sannan kuma wasa yana kyautata kwakwalwar yaro yana bude masa tunani; shi ya sa ma Allah (S.W.T) a littafi mai girma yake cewa: “Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa, kuma lalle mu masu tsaro ne gareshi”[4]. Wani lokaci wasannin har da na kwamfita, amma kada a rika sanya masa na harbe-harbe da duk wasanni da malaman tarbiyya suka yi umarni a nesantar da yaro daga gare su domin yawancinsu sukan kashe wa yara tausayi.

Idan ka haramatawa yaranka wasannin yara kana cutar da shi ne, domin wani lokacin yakan dakushe wa yara tunani, sannan yakan iya haifar da dabi’ar son ramuwar abin da ba su yi ba na wasannin yara. Mutum har ya girma yana bukatar yin wasanni sai dai yakan sassaba ne tsakanin manya da yara da kuma kasancewar dalilin da yakan sanya kowannensu yin wasannin yakan sassaba, shi ya sa yaro har ya zama saurayi ana son ya rika wasanni kamar wasan kwallo da sauran wasanni na motsa jiki.

Kuma yana kan hukuma ne a kowace unguwar dole ne ta samar da wajan shakatwa da wajan wasannin yara da filin kwallo da sauransu, amma abin takaici a kasashenmu haka a kan samu mayun filayen wasannin jama’a ta yadda ita hukuma ba ruwanta da jin dadin al’umma, sannan kuma da za a ware filin da an samu wani maciyin amanar al’umma ya hau kan kujerar mulki sai ka gan shi yana lasar baki yana hadiyar yawu shi ya ga wani babban fili, idan ba a dauki mataki kwakkwara ba yanzu ka ga mayen filin ya kama kurwar wannan fili ya raba shi ga mutane ya sayar.

Kashe Azamar Yara

Daga cikin miyagun halaye da kan iya rusa himmar yaro da azamarsa da kuzarinsa har ma da kwakwalwarsa shi ne tsorata shi, da kyamarsa, da kushe shi, da muzguna masa, da sukansa, ta yadda za a sanya masa tunani da yakan kai shi ga jin shi ba ma mutum ba ne, ko kuma ba shi da hakkin bayyanar da ra’ayi. Haka nan takura shi ko bakanta masa rai da dukansa ba ji ba gani. Wadannan abubuwa ne da sukan sanya shi ya ji cewa ashe shi yana bukatar ya girma domin ya zama mutum ya shiga sahun manya don ya huta da wannan nau’oi na azaba da gallazawa, ko ya sanya shi fadawa hanya ta banza ko ta daukar fansa da kece rene. A nan ne idan ya fusata kuma ya samu masu karbarsa kowane irin mutane ne sai ya mayar da su abokansa ya kuma tasirantu da su.

Irin wanann nau’i na tarbiyya ba komai a cikinta sai danne hakki na dan Adam da kuma rusa manyan gobe na al’umma wanda mun riga mun yi nuni da irin miyagun abubuwa da hakan kan iya haifarwa.

Ba A Yi Wa Yaro Mugun Fata

Saudayawa wasu iyaye sukan yawaita tsine wa yaransu da mummunan zagi da kan iya kara wa yaro lalacewa, abin da hatta da wasu abubuwan kamar dukiya da ta hada da tumaki, da kaya, da gida, da tufafi, da abin hawa, an hana la’antar su don su zama abu mai alheri ga al’umma kamar yadda akwai Hadisai da suka zo na haramcin miji ya la’anci matarsa, mu sani wannan ba abin da zai kara wa yaro sai kekashewa da kangarewa da lalacewa.

Da yawa zaka ga mutane da dama maimakon su yi wa yaronsu addu’a da za ta gyara shi sai su yi ta yi masa mugun baki da mummunan fata, abin da wahalarsa da tasirinsa zai dawo ga iyaye a karshe domin idan wannan tsinuwa ta bi shi ya lalace ba abin da zai same shi a duniya sai talauci, da rashin albarka a kan duk abin da ya sa a gaba. Kuma ka bincika rayuwar irin wannan yara da kullum iyaye kan tsine musu ka gani zai wahala ka ga dayansu wanda ba ya fama da talauci ko tabarbarewa kan duk abin da ya sa gaba, saboda haka ya kamata su sani idan ya lalace su ne na farko da abin zai fara shafa.

Ba A Hana Yara Wasanni[5]

Wasu mutane ko wasa suka ga yara suna yi to sai tsawa da zagi kamar ba a sha karantawa ba a Surar Yusuf: “Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa, kuma lalle mu masu tsaro ne gareshi”[6].. Saudayawa su yaran sukan sauwara irin wadannan mutane a kwakwalwarsu a matsayin mugwaye masu takura musu ko a matsayin makiyansu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next