Kurkuku Bincike Da Hukunci



·   Ba wa wanda ake tuhuma hakkin sanya kayan da suka ga dama ba dole sai unifom din furzin ba. Da kuma hakkin yin aiki ko kasuwanci da aikin albashi, da yiwuwar a rika kawo masa abinci daga gida ko a rika sayo masa da kudinsa. Haka nan hakkin mallakar littattafai da kayan rubutu da kula da lafiyar tsaronsa.

 

MAHANGAR MUSULUNCI

Mas’alar magana kan Gidan Sarka ta mahangar Musulunci tana da ‘yar sarkakiya kuma akwai ra’ayoyi masu bugun juna kan haka saboda haka wanda yake son jin ra’ayi na karshe sai ya ji daga bakin wanda yake yi wa takalidi kamar Maliku, ko Shafi’i, ko Hanafi, ko Hambali, ko Ahlul Baiti (A.S). Amma Gidan Sarka a musulunci shi ne: Iyakance mutum da hana shi walwala da tasarrufi na musamman ba tare da kebantace haka da wani wuri na musamman ba, muhimmi shi ne hana shi wannan zirga-zirga ta musamman, don haka ma ya kasance Gidan Sarka a musulunci ana tsare mutum a gidansa ne ko unguwar da yake ya zama ba ya iya fita nesa da ita. Shi ya sa furzin a musulunci ya zama ana tsare mutane a masallaci ne ko kuma a gidansa ko wani gida, ko ta hanyar wakilta wani da zai rika bin sa duk inda za shi kamar yadda wani hadisi ya kira shi da sunan ribataccen yaki (Asir) saboda wannan[1].

Hakan nan Gidan Sarka ya kasance a lokacin Manzo (S.A.W) da Abubakar, har sai da ya kasance lokacin Umar Dan Khaddabi, sai ya sayi gidan Safwan Dan Umayya da dinare dubu hudu ya sanya shi ya zama Gidan Sarka da ake tsare mutane a ciki, wannan shi ne Gidan Sarka na farko da aka kirkiro a Musulunci, domin haka ne malamai suka kasu gida biyu; Masu ganin cewa aikin sahabi hujja ne koda ya saba da Manzon Allah (S.A.W) sun kafa hujja da aikin Umar, wadanda suke ganin sunnar Manzo (S.A.W) ba ta shafuwa da aikin sahabi saboda shi Allah ya aiko kuma Allah ya fi kowa sanin maslahar bayinsa shi ya sa ya aiko manzonsa da wannan sako kamar yadda yake kuma ba ya karbar canji sun ta fi a kan kasancewar kurkuku bisa tsarin duniya a yanzu da yake daidai da sunnar Umar da cewa ba hujja ba ne, domin Allah (S.W.T) ya aiko Manzo ne (S.A.W).

Wata kasa daga kasashen Turai a kwanan nan ne ta fara dawowa kusan samfurin furzin a musulunci, ta yadda tsarin Gidan Sarka ya zamana ta hanyar hana mai laifi fita daga gidansa ne, sai ya zauna cikin iyalinsa a tare da shi akwai wani inji kamar agogo da a kan sanya shi a hannu ko kafarsa da duk inda za shi abin yana iya nunawa ta kwamfitar jami'an tsaro cewa ya fita yawo, wato ya saba doka kenan, kuma a kan haka suna iya yi masa wani hukuncin. Koda yake a Musulunci ana son karfafa ruhin mutum ne ta yadda shi da kansa in an bar shi da kansa ba zai saba dokar Allah ba kamar yadda azumi kan koyar da irin wadannan darussa, amma wannan ba ya hana mu kawo irin wadannan abubuwan a matsayin misalai.

Kamar yadda ya kasance ba a tsare wanda ake bi bashi a lokacin Manzon Allah (S.A.W) da Abubakar da Umar da Usman da Ali (A.S), wannan al’amari ne da Alkali Shuraihu ya kirkiro shi, shi ya sa a wajan malamai aka sake samun sabanin halarcin tsarewa saboda bashi da hujjar cewa aikin Alkali Shuraihu ba hujja ba ne, al’amarin bahasi ne mai kama da na sama da muka ambata, sai dai ya fuskanci sabani mai yawa da yake bukatar bincike.

Babu wani daga musulmi da ya halatta yin furzin kamar yadda yake a yau da wannan yanayi da za a tara mutane da yawa a gida daya suna ganin al’aurar juna, kuma ga kunci, har ma ya zama ba su iya yin alwala ko salla ko ma babu wurin yin su, zafi da sanyi yana cutar da su, har ma ana iya tsare wani shekara daya ba shi da wani taimako ko ma asali an tsare shi ne a kan bashi, kamar yadda a lokacin Halifa na biyu (R.A) aka fara kashe mutane biyu ko sama da haka don sun kashe mutum daya, wanda wannan ya saba da hukuncin da Manzon Allah (S.A.W) da na Halifansa na farko suka tafi a kai, na cewa, ba a kashe mutum biyu don kashe mutum daya sai da diyya[2].

Saboda haka a tsarin Musulunci wuri ba shi ne furzin ba, abin da yake furzin shi ne; hana tasarrufi na musamman wanda yana iya yiwuwa a ko’ina ne kuma a kowane waje kamar masallaci ko gidan mutum cikin iyalansa[3] wanda wata kasa ina tsammanin suwizlanda ce kamar yadda gidan Talabijin /Rediyon IRNA ya shelanta a wannan kwanakin sun fara daukar irin wannan usulubin da Manzon Rahama ya zo da shi domin shi ne ya fi dacewa da ‘Yan Adamtaka.

Kamar yadda muka sani Gidan Sarka a wannan zamani ba komai ba ne sai take hakkin dan Adam da zaluntarsa ba bisa hakki ba, kamar yadda aka yi sabani a kan cewa, shin Manzo ya taba tsare wani mutum? Yayin da malamai suka tafi a kan cewa ya taba tsare wani mutum saboda tuhumarsa da ake yi da kisan kai har sai da aka gama bincike. Kamar yadda furzin yana iya zama ta hanyar sanya wani yana bin bayan tsararre duk inda za shi, misalin haka wanda ake bi bashi ya ki biya kuma mai bin sa bashi ya san yana da shi, sai shari’a a kotu ta ba shi dama idan yana da bawa ya sanya bawansa ya rika bin bayan mai taurin bashin duk inda za shi, kamar yadda hakan ya faru a lokacin Annabi (S.A.W). Haka nan muna son mu kara haske a kan cewa, furzin a musualunci ba ana yin sa domin huce haushi ba ne kan masu laifuka, a’a, ana yin sa ne domin ladabtarwa da kuma gyara masu laifukan da kuma gyara halayensu da ilimantar da su da sanar da su hakkokinsu da kuma wadanda suka hau kansu.

 

HALARCIN YIN FURZIN (TSARE MUTUM)

Kamar yadda yake sananne cewa furzin a Musulunci abu ne wanda ya halatta a yi shi da ma’anar da muka fada a sama da Karin cewa, wani lokaci ya hada da kora daga gari shekara, ko kuma ta hanyar hana kowa ya yi magana da shi, ko ta hanyar umarninsa da kada ya sake kusantar matarsa, ko kuma a hana duk dangi da na nesa su yi masa magana zuwa wani lokaci mai tsayi ko maras tsayi daidai yadda shari’a ta tanada, ko kuma hana a sayar masa komai kuma kada a saya daga gare shi, kamar yadda tsarewa tana iya yiwuwa a gidan wanda aka yi wa laifi ko gidan mai laifi daidai gwargwadon laifi da nau’insa da kuma izinin da shari’a ta bayar, kamar yadda wani lokacin ana tsare mutum a gidansa daurin rai da rai kamar wacce ta yi zina tana da aure, koda yake an shafe wannan da jifa, amma wanda ya rike wani, wani ya zo ya kashe shi, shi har yanzu yana da wannan hukuncin, da makamancin haka.

Karin haske a kan haka shi ne akwai wasu mutane da aka halarta tsare su ba don suna da laifi ba sai domin dabi’arsu da kan iya kai su ga lalacewa idan sun fita, wasu daga cikinsu sun hada da matar da take da sha’awa da yawa da ake tsoron fasadi gareta ko kuma wacce akwai tsammani mai karfi na tana iya aikata irin wadannan ayyuka, kamar yadda Abu Abdullahi Assadik (A.S) ya umarci wani mutum da kada ya bari a shiga wajan babarsa kuma kada ya bari ta fita waje ita kadai[4]. Daga irin wannan akwai tsare fasikan malamai da jahilan likitoci da mai taurin bashi da ya ki biya alhalin yana da shi. Kamar yadda ba dauri na rai da rai sai ga mutane uku: Wanda ya rike wani don a kashe aka kuma kashe shi, da mace mai ridda daga Musulunci har sai ta tuba, da barawo bayan yanke ‘yan yatsun hannun dama, da ‘yan yatsun kafar hagu, har sai ya tuba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next