Kurkuku Bincike Da Hukunci



Duba ka gani mana ribatattun yaki a lokacin Manzo (S.A.W) duk da suna da hukuncin kisa a kansu amma sai aka raba su a gidajen Sahabbai, kuma kowane Sahabi yana ciyar da su da kuma ba su duk abin da yake ci ko yake amfani da shi ne, kamar yadda wasu an tsare su a gidan wata mata daga Bani Najjar ne[11].

Haka nan bai halatta dan furzin ya rika fita wasu wurare ba domin in ba haka ba sai ya zama ba shi da bambanci da na sake, sai dai yana iya sallar juma’a da idi kamar yadda yake a tsarin Musulunci, kuma bisa kula da tsaron kada ya gudu ko kuma da lamuncewa daga waliyyansa. Amma sauran fita waje ba a ba shi izininsu ba, kamar fita zuwa gaida maras lafiya ko raka jana’iza ko taron mutane. Amma ba a hana shi ciniki da saye da sayarwa ba da aiki da kyauta da sadaka da makamancin wannan, kamar yadda ba a hana matarsa da danginsa zuwa wajansa ba, kuma ba a hana kebanta tsakaninsa da matarsa ba har ma da kusantar juna, sabanin yadda furzin yake a dokar mafi yawancin kasashen duniya a yau, domin hana miji da mata kusantar juna yana haifar da bala’i mai girma kuma saudayawa yakan kai ga rabuwar aure, kamar yadda wani mutum ya nema daga imam Ali (A.S) a tsare su tare da matarsa bayan matar ta kai karar rashin ciyar da ita da ba ya yi domin cutar da ita, sai imam (A.S) ya ba shi damar haka ya tsare su tare a gida daya ya kuma ba matar izinin ta zauna tare da shi a gidan tsarin kamar yadda ya nema[12]. Na ce: Wala’alla mijin ya nemi haka ne domin gudun kada matarsa ta fitinu da wasu kuma ta yarda ta zauna da shi a furzin din (wannan ba yana nufin ita ba ta da ikon yawo ba ne ko fita waje da izinin mijin nata ba) ko kuma shi mijin yana tsoron kada shedan ya kai shi ga lalacewar dabi’a kamar Istimna’i da makamantansu[13].

3.   Biya idan mai tsaron furzina ya yi masa barna

Idan mai tsaron furzina ya yi masa barna kamar ya yi sakaci da lafiyarsa ko abincinsa ko maganinsa ko sauran kayan rayuwarsa, kamar kayan sawa na sanyi sai ya yi rashin lafiya, ko ya mutu, to dole a yi masa kisasi ko ya biya diyya idan bisa kuskure ne.

Sheikh Tusi da Abu Hanifa suna cewa: Idan ya tsare yaro bisa zalunci sai gini ya fado masa ko zaki da damisa da makamantansu suka kashe shi ko maciji ya harbe shi ko kunama sai ya mutu to dole ya biya diyyarsa[14]. A sani a wannan mas’alolin akwai rassa masu yawa da wannan dan karamin littafi ba zai iya kawo bayaninsu ba.

4.   Kula da al’amuran addinin ‘yan furzin

Yana kan shugaba duk ranar Juma’a da ranar idi ya fito da ‘yan furzin zuwa sallar Juma’a da ta Idi, idan sun gama salla sai a mayar da su furzin. A nan ana iya wakilta ko wani dan furzin da danginsa da lamuncewar ba zasu bari ya gudu ba, kuma bayan salla su dawo da shi, ko kuma Daula ta dauki nauyin hakan ta hanyar ‘yan sandanta

 

MUTANEN DA SHARI’A TA HUKUMTA A TSARE SU

Ya zo a littattafan Mazhabin Ahlul Baiti (A.S) da na Sunna ruwayoyi da suke nuna mutanen da shari’a ta yarda a tsare su kamar haka:

Wanda ake tuhuma da kisa kwana shida har a gama bincike, idan kwana shida suka cika waliyyan wanda aka kashe ba su da wata hujja to za a sake shi ne.

1.     Fasikan Malamai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next