Kurkuku Bincike Da Hukunci



A Amerika da Rasha kawai kusan yawan ‘yan sarka ya kai kashi 700 a cikin kowane mutane 100, 000 masu zaman kasashen, amma a Ingila da Wales suna da wajan kashi 125 ne, na kasar Sin (Cana) kuwa 110 ne, kashi daya cikin uku na sauran kasashen duniya kuwa suna da 150 ne ko sama da haka cikin 100, 000 wanda yawancinsu kasashe ne na Afrika Ta Kudu ko Karibiyan ko Asiya Ta Tsakiya da kuma Tsakiyar da Gabashin Turai

A Rasha an yi bikin cikar shekara 55 da sakin fursunonin Kasar Jamus sama da 120, 000. Haka nan Gidan Sarkar Butyrsky na Masko (Moscow) a cikin shekara 20 ya dauki mutane 5,500 a sel dinsa wanda aka gina domin mutane 2,500 amma saboda cutar nan ta annobar Tuberculosis a tsakanin fursunonin duniya kamar yadda masanin magunguna Sans Frontières (Doctors Without Borders) ya siffanta a matsayin hadari da yake fuskantar ‘yan Gidan Sarka wanda yake barazana ga lafiya a duniya.

A kasar Koriya Ta Kudu an saki ‘yan fursuna 3, 586 domin murnar samun ‘yan ci daga Kasar Japan a 1945 haka ma a Kasar Pakistan aka saki 20, 000. A kasashe da dama a kullum al’amarin fursuna yana dada tabarbarewa ne, halinsu yana dada muni, misali a Afrika Ta Kudu Fursunoni a gwamatse suke, kamar yadda a Kasar Tailand (Thailand) sama da mutane 200, 000 ake tsarewa a wajan da aka gina domin tsare mutane dubu 80, 000, kamar yadda a kasashen Latin Amerika kusan haka nan ne.

A kasar Ceks (Czech) wajan mutane 19, 500 ake sanya mutane 24, 000 ga kuma yunwa da hali maras kyau da ke damun tsararrun. A Peru kuwa an yi yamutsi da ya jawo kashe fursuna biyar a babban furzin din kasar Peru wato Lurigancho ga shi kuma wajan mutane 6, 000 ne ake sanya mutane 15, 000. Haka nan komitin gano laifuffukan furzin da take hakkin fursuna ya gano laifuffuka manya na take hakkin fursuna a duniya da ya hada da azabtarwa da kisa da batarwa a matsayin manyan laifuffukan take hakkin fursuna. A shekarar 2001 yawan fursuna a duniya ya wuce sama da miliyan Takwas.

Mazauna murabba’in Kasar Amerika duk mutane 100, 000 mutane 702 daga cikinsu ‘yan furzin ne. Haka nan aka samu raguwar yawan fursuna a Kasar Rasha da kuma Kasar Afrika Ta Kudu zuwa 465 da kuma 385 yayin da na kasar Sin ya zauna kamar yadda yake da kashi 112. Amma a Turai fursuna a Ingila da Wales ya tashi zuwa 128 al’amarin da ya sanya suka zama sun fi kowa yawan fursuna a kan sauran kasashen Turai, yayin da adadin kasar Potugal ya zauna a 127 na Finland kuma 52 Irelanda ta Arewa kuma 60 Denmak kuma 61 wadanda su suka fi karancin fursuna a Turai.

Kasashe da dama suna da niyyar karanta adadin fursuna, Sarkin Bahraini ya shelanta afuwa ga fursunan siyasa 400 wadanda aka kulle su a shekarar 1990s. A Malawi Baliki Muluzi ya saki fursuna 880 a ranar bikin kasa kamar yadda aka saki 40, 000 a kasar Kazakhstan don girmama bikin cikar shekara goma na samu ‘yan cin kasa.

A Kyrgyzstan kuwa an yi afuwa ga 5, 000 kamar yadda a Rasha aka karfafi rage fursunoni kusan 300, 000 ta hanyar bayar da beli da makamantan haka. Zalunci da mutuwa da cututtuka sun yawaita kwarai a fursunonin duniya, kusan mafi muni a ‘yan kwanakin nan shi ne a binda ya faru a kasar Barazil da ya kai ga mutuwar sama da fursuna ashirin da kuma garkuwa da kusan 8, 000. Kamar yadda a kasar Chile aka samu mutuwar sama da 26 saboda lalacewar wutar lantarki da ta haddasa gobara.

A kwai kuma mummunan mace-macen fursunoni a kasashen Afrika saboda rashin kula, kamar yadda aka rawaito cewa a Maroko akwai mummunar dabi’ar nan ta cin hanci tsakanin masu kula da furzin da takurawa da cututtaka da kuma laifukan jima’i ga kananan yara. A kasar Malawi akwai yaduwar cututtuka da cunkoso a fursunoni da kuma yaduwar cututtukan da a kan dauka. A kasar Mozambik fursunoni 83 ne suka mutu saboda yunwa da kishirwa a shekarar 2000 yayin da sama da 120 a kan sanya su a cell mai fadin 21 sq m (226 sq ft). A Afrika Ta Kudu fursuna yana samun karancin iska mai lafiya da ruwan sha mai kyau wanda ya janyo barkewar malariya da ta shafi fursunoni 600 (dari shida)

Matsaloli da sukan faru sakamakon cunkoso a furzin da kuma wacce yanayi maras kyau kan jawo suna damun kasashe da yawa na turai al'amarin da ya kai kusan fursunoni 100, 000 suke fama da tuberculosis, kamar yadda Bankin duniya ya bayar da rancen Dala ($) miliyan 50 domin maganin cutar kanjamau da take damun fursunonin da suka kamu da ita.

A kwanakin bayan nan kusan fursononi 250 suka yi yajin cin abinci a kasar Turkiyya na kusan kwana talatin saboda tsananin matsi da neman hakkinsu na rashin kawo sababbin fursunoni furzin din. Amma wani abu mai kayatarwa da nuna tausayi da ya faru shi ne a Kasar Iran a yau ranar Talata 9/10/1382 daidai da 6/11/1424, Kuma daidai da 30/12/2003 ne, aka yafewa fursunonin da danginsu suka mutu a girgizar kasar da ta faru a garin “Bam” na yankin Jahar Kirman a ranar Juma’ar da ta gabata da ta kashe kusan mutum dubu hamsin koda yake wasu rahotannin sukan ce : Sama da mutane dubu ashirin.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next