Kurkuku Bincike Da Hukunci



 

HUKUNCIN KISA

Magana game da fursunan da yake jiran hukuncin kisa a kasashen duniya tana bukatar littafi na musamman saboda haka ba zamu tsawaita a kan ta ba sai dai mu ce: Kusan gaba dayan kasashen duniya suna da hukuncin kisa a yau a bisa laifuffuka na musamman daidai da dokoki na kasar da kuma hukuncin kotuna. Haka nan Magana game da adadin mutane da ake kashewa a kowace kasa da hanyoyin da a kan bi suna da Magana mai tsayi da littafinmu ba zai iya dauke wa ba.

Amma muna iya cewa a shekarar nan a kasar Sin an zartar da hukunci a kan sama da mutane 801 kamar yadda a Amerika aka kashe 89 a shekarar 2000 amma a shekarar da ta biyo baya an kashe 66 daga fursunoni ne kamar yadda Kungiyar Afuwa Ta duniya Ta shelanta.

 

TARA

Mafi saukin caji da a kan yi wa masu laifuka a duniya wanda ya yadu a ko'ina a duniya shi ne tara musamman ga direbobi da laifunsu yakan faru a cikin kowane sakan, a kasar Farisa kwanannan suka kara kudin tara ga diribobi da Karin tsanantawa ga wanda ya ki biya kan lokaci saboda yawan hatsari da yakan faru sakamakon ganganci ko rashin kwarewa ko saba dokar tuki, kusan a ranar Alhamis 6/9/1382 H.Sh. Wato 2/10/1424 H.K. daidai da 27/11/2003 M. a hanyata ta tafiya Tehran zuwa bikin cikar sati biyu da haihuwar 'yar Muhammad Amin mai suna Ummu Abiha, (bikin ba a yi shiba a satin farko saboda ya fada cikin azumi ne) an yi hatsari kusan 48 tsakanin birnin Tehran da Kum da suke da nisan kilo mita kusan 130 a tsakaninsu, kamar yadda Alhamis mai zuwa na sake yin kwantankwacin tafiyar tsakanin garuruwan biyu kuma na sake ganin an yi hatsari kusan makamancin wannan adadi har abin yakan ba ni mamaki saboda ya yi yawa, sai direban motar da nake ya ce: Da ya fi haka shi da bai yi mamaki ba musamman ga shi an yi ruwa kuma mutane ba sa rage gudu kuma suna gudu dab da juna, ya ce: Ai idan ya fi haka ma kada ka yi mamaki.

Kusan a Ingila kashi 42 na caji da ake yi wa masu laifi da ya hada da masu tuki ta hanyar tara ne. Tara laifi ne ko kuma in ce caji ne da ba shi da abin kunya kuma ba ya zubar da mutunci, ba kamar shiga Gidan Sarka yake ba da yakan zubar da mutunci ko kuma ya jawo rasa aiki domin wasu ma'aikatu sukan hana wanda ya taba yin zaman kaso aiki sai da kyar.

Haka nan tara tana da wahala ga talaka idan ta wuce karfinsa, sai dai wasu kasashe sun yi maganin wannan ta hanyar buga tara din ko cin tarar bisa la'akari da abin da wanda aka buga wa tara din yake samu a wata ko shekara. Kuma saudayawa a kan kai mutane kotu sakamakon kin biyan tara wanda shi ma wani laifi ne na musamman da yakan iya kai wa ga tsarewa sati biyu ko kasa da haka da kuma wata tarar da tana iya fin ta da yawa ko kuma a ninninnka wancan ta farkon tare da tsarewa, amma a wasu kasashe saudayawa bayan an caji mai laifi a kan kuma kara tarar da kuma tsarewa to ana sakinsa koda bai kai kwanakin da aka yanke masa ba matukar kafin su cika an biya tarar.

Magana kan tara da yawanta a duniya da gwargwadonta da kuma abin da takan jawo na tasiri ko rashinsa mun wakilta maka shi ga manyan littattafai sai ka duba can.

 

CI GABA A NAU’IN GIDAJEN SARKA

A duniya a kan daure fursunoni a nau'in wurare daban-daban ne wasu wuraren ba su da kyau da sukan sanya yaduwar cututtukan da ba kawai suna shafar fursunan ba ne, a’a, har ma da matsu tsaron Gidan Sarka din, misali a Ingila a kan samu yaduwar cututtukan da har masu gadin furzin sukan shafa ba kawai dan Gidan Kason ba, a yau a gidajen sarka ana tsare mutane ne daidai shekaru da kuma jinsi mata da maza a ware sabanin wasu wurare da ana tsare maza da mata a wuri daya ne ba tare da la'akari da jinsi ko shekaru ba, al'amarin da yakan kai ga yaduwar "Zazzabin Gidan Sarka" da kan kashe ba kawai fursuna ba har ma da matsu tsaron su.

Da yawa daga fursononi a yau a kasar ta Ingila ana tsare su ne a kan ruwa cikin tekuna da koramu kamar kogin nan na Thames da sauransu a cikin tsofaffin jiragen ruwa, an ce suna ma jiran a kai su kasar Austaralia a cikin jiragen amma aka saki wasu kafin su fara tafiya.

Wanda yake son Karin bayani ya nemi littafin nan na John Howard mai suna "The State of the Prisons in England and Wales" (1777) ya sha mamaki!. Tsarin furzin a Amerika ya fi ban mamaki musamman wadanda aka yanke wa hukunci karkashin gwamnatin kasa.

 

DAMUWADA KUMA HALIN DAN FURZIN

Damuwa game da halin fursuna ba ta ragu ba a duniya kuma haka nan aka gono irin mugun zalunci da wasu fursunonin kan sha a hannun wasunsu a sakamakon mugun cunkoson da a kan samu a gidajen sarka, kamar yadda kullum adadin 'yan Gidan Sarka daduwa yake a duniya. Duk da canje canje da ake faman yi a kasashe daban-daban a duniya game da raguwar laifuffuka da yawan fursunoni amma abin ya ci tura a kullum sai karuwa suke yi, alal misali, duba yawan fursunoni a Ingila tun shekarun bayan yakin duniya na biyu zuwa yau ka ga ni. Kamar yadda yawanci masu laifi a duniya wadanda suka fi yawa a furzin maza ne, koda yake yanzu yawan mata a duniya masu laifi da ake tsarewa ya fi na maza saurin daduwa da karuwa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next