Kurkuku Bincike Da Hukunci



3. Mai ila’i idan ya ki komawa matarsa bayan wata hudu da kuma komawa kotu amma ya ki, to sai a tsare shi sai ya saki tilas ko ya koma mata.

4. Wanda ya rike wani mutum wani kuma ya zo ya kashe shi. To shi wanda ya yi rikon ana daure shi rai da rai kuma a rika yi masa bulala hamsin kowace shekara.

5. Wanda ya umarci wani mutum da (ba bawa ba) ya kashe wani mutum.

6. Bawan da ya yi kisa da umarnin ubangidansa.

7. Wanda ya sa mai kisa ya gudu daga hannun waliyyan wanda aka kashe, ana tsare shi har sai lokacin da aka kama mai kisan ko ya biya diyya ko kuma idan sun yafe.

8. Dan fashin da bai kashe kowa ba, bai kuma dauki dukiya ba, domin da ya dauki dukiya za a kara masa hukuncin sata a kai.

9. Mai suranta gumaka yana sayarwa, amma idan bai tuba ba, kuma tsare shi ne zai yi maganin ci gaba da haka. Wannan idan mun ce yin gumaka a wannan zamani da ake yin su domin ado haramun ne, domin wasu sun tafi a kan cewa hikimar haramta su a wancan lokaci saboda tsoron kada a bauta musu ne wanda wannan al’amari a kasashen musulmi babu haufinsa. Amma mun zo da wannan a matsayin misali ne amma in ba haka ba wannan hukunci ya hada da duk wani hukunci na mai fasadi da bata mutane da tsari ne kawai zai tsayar da shi.

10.  Mai duba: Wanda yake gaya wa mutane abin da zai faru a kansu ta hanyar duba taurari da bugun kasa da makamantansu.

11.  Wanda ya kusanci ‘yar’uwarsa aka yi masa bulala dari amma bai mutu ba, to ana tsare shi.

A kasashenmu akwai abin da ba nau’i ne na furzin ba amma ya yi kama da furzin wanda wannan take hakkin dan Adam ne, kamar takura kananan yara, ko kuma mai motar haya ya rika sanya mutane da yawa a layin kujerar mota ta yadda har lumfashinsu yana daddaukewa, wannan wasu abubuwa ne da ya kamata a bar su domin yana iya kaiwa ga cutar da al’umma da kuma takura su, kuma mutanenmu suna cewa zafin nema ba ya kawo samu. Irin wadannan abubuwa suna da yawa sai dai babu damar yin magana a kansu a cikin wannan takaitaccen littafin.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next