Kurkuku Bincike Da Hukunci



Kuma haka nan samari sun fi tsofaffi yawa kamar yadda yawancin 'yan Gidan Sarka sun yi wani laifin kafin wanda aka daure su kuma aka sake daure su bayan sun kara yin wani laifin, haka nan yawancin wadanda ake tsare da su a duniya laifuffukansu sun fi yawa a zaluntar wani ta karfin tsiya da fyade ko sata da fashi.

 

‘YAN FURZIN DA NAU’IN GIDAJEN SARKA

Gidajen sarka iri iri ne kuma ama gina su ne ta yadda na ciki ba kasafai yake ganin abin da yake wajen Gidan Sarka ba, koda yake wasu kasashen sukan sanya waya ta yadda idan na ciki ya fita daga dakinsa yana iya hango titinan gari da duk abin da yake kewayensa, wani lokaci Gidan Sarka yana zama a ruwa a cikin jiragen ruwa kamar yadda ya gabata game da kasar Ingila. Kuma yawancin kasashe in banda kadan daga cikinsu ba sa ware tsakanin tsofaffi da yara a Gidan Sarka, wasu ma har tsakanin maza da mata.

Amma tambaya a nan shi ne? Shin ana tsare mutum ne domin gyara da kawar da lalacewarsa ko kuma kawai domin azabtarwa ne? Wannan shi ne mafi girman bala'in da gidajen sarka suke fama da shi a duniya ta yadda ba a damuwa da tarbiyyar na furzin. A kan haka ne ma kasar Farisa take kokarin samar da laburare da dakin hardace kur'ani da koyan sana'o'i ga fursunoni, ta yadda kafin fursuna ya gama zaman kaso ya san wani abu daga ilimi. Kamar yadda a duniya wasu wurare suna da Gidan Sarka budadde da a kan ajiye wadanda aka san ba zasu gudu ba ko kuma laifinsu karami ne sosai, wato su ba hadari ba ne ga al'umma.

Sa'annan saudayawa a kan kasa Gidan Sarka zuwa babba da karami da kuma wanda ake daure masu hukuncin shekaru masu yawa da na masu shekaru kadan, ko kuma na masu laifin kisa da makamantansu da na masu laifi matsaikaci ko babba. Wato a kan kasa wani lokaci daga kan wadanda suke hadari kuma suna iya guduwa zuwa wadanda ba su da hadari kuma ba sa iya guduwa wadanda ana ba su tsaro maras muhimmanci ne.

A takaice muna iya cewa Gidan Sarka waje ne da a kan tsare mutane a ciki da hadafi daban-daban da yawanci ba sa kai wa ga gyaran dan Adam a yau, a sakamakon yanayin tunanin su masu tsare fursuna da kuma masu tsaron gidajen sarka din da ba sa ganin mutumin da aka tsare a matsayin mutum balle su yi wani tunani na ganin gyaransa, hasali ma yawancinsu ba su da tarbiyya da zasu iya ba wa dan Adam kuma ba su da insaniyya da mutuntaka, yawancinsu sukan ga tsararre kamar dabba ko kasa da haka, al'amarin da ya sanya babu wani mutum da ake take hakkinsa a duniya irin dan Gidan Sarka. Shi ya sa da zaka duba yanayin abinci da rayuwar yau da kullum na fursuna, hatta da lokacin tashi daga bacci ko kuma zama ko wanka da sauran al'amuransa duk suna karkashin tasaruffi da kula ne. Ta haka ne da sunan kula aka tauye mafi yawan hakkin 'yan Gidan Sarka, kamar yadda yawanci suna da kayyadadden lokacin da ake iya ziyartar su, kuma a wasu Gidajen Sarka din ba a yarda su yi Magana baki da baki da mai ziyarar su sai ta talpon da ana iya ganin su ta gilas ne kawai, wani abin mamaki wannan irin tauye hakki na dan Adam wasu sun dauka ci gaba ne!

A wasu kasashe hakkin ziyara duk sati hudu ne sannan kuma mai Magana da dan Gidan Sarka zai zama a gaban dan sanda ko shugaban furzin, sannan kuma masu ziyartar dole ne su zama na kusa da shi kamar uwa ko uba ko 'yan'uwa da makamancin haka. Kuma da wani abu zai sanya sai ya je kotu kamar sakin matarsa misali sai dai wani ya wakilce shi, wato shi ba a bari ya je, haka nan ne ake mu'amala da dan Gidan Kaso kamar mafi munin halitta da Allah ya halitta a bayan kasa.

A wasu jahohi na Amerika a kan bari iyalansa su zo su zauna da shi kwanaki masu dama kamar sati, amma a Ingila babu wannan doka kuma ba shi da ikon rubuta sama da wasika daya a sati, malam duba ka ga yadda dan Adam yake a duniya kamar shi wanda yake sanya dokokin shi ne Ubangijinsa. A kwai Magana mai yawa game da fursuna da laifuffuka kamar neman gudu da dukan masu tsaro da barin wajen da aka umarce shi da ya tsaya da makamantansu da laifinsu a duniya wato sakamakonsu sai a duba manyan littattafai kan hakan.

 

HAKKIN DAN GIDAN KASO

Kasashen duniya har yanzu ba su yi wani abin a zo a gani ba game da hakkin 'yan Gidan Sarka ba, kuma yawanci ba ganinsu ake kamar wasu mutane ba, saboda haka duniya har yau ba ta yi wani abin a zo a gani game da hakkin su ba, wasu kasashe a rubuce sun yi gyare gyare amma a aikace sai abin da ya yi gaba.

Wani lokaci a kan samu matsala tana tasowa daga fursunoni amma yawanci hakan yakan faru ne sakamakon cunkoson Gidan Sarka ko takura ko rashin sa ido da kula da halinsu. Kamar yadda wasu lokuta wasu fursunonin sukan sha baker wahala a hannun 'yan'uwansu 'yan Gidan Sarka, musamman ma masu karancin shekaru a cikinsu ko wadanda suke da wani laifi na musamman kamar yadda masu laifin fyade sukan sha a hannun wasunsu a Ingila ko kuma wadanda aka tsare saboda cin rashawa, kamar yadda a kan samu matsalar kabilanci a wasu gidajen sarkar na wasu kasashe da yakan kai ga rigima ko kuma rigima kan yadda za a tafiyar da Gidan Sarka. Kamar yadda a wasu kasashe a kan bayar da sakamakon shekara na yadda gidajen sarka suke da kuma matsalolinsu da yadda za a magance ta.

 

DAWO DA HAKKIN MUTANE KO BIYAN DIYYA

Saudayawa a kan shigar da wasu furzin saboda sun kasa biyan diyya ko hakkin wasu mutane na musamman, a kasashe daban-daban suna da tsari da ya shafi hakan, wani lokaci a kan tsare wanda ya kasa biya ko kuma a bar shi ya ci gaba da neman abin da zai biya bashin da yake kansa, saudayawa wannan yakan sanya a kyale shi a kan wannan sharadi. A tsarin musulunci wanda ba ya iya biya ba shi da waliyyai da zasu biya a kan biya irin wannan daga Baitul mali, Daula kuma tana iya yi masa ukuba daidai gwargwadon gangancinsa ko barnarsa, kuma hakan yana daga cikin tsarin wasu kasashen a rubuce duk da wajan aiki a kan samu matsala. Da yawa a wasu kasashen kotu takan wawure hakkin wani da a kan biya da sunan hakkin kotu, amma wannna ban sani ba shin daga dokoki ne ko daga san ran masu yanke hukuncin kotu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next