Kurkuku Bincike Da Hukunci



4.   Mai ila’in da ya ki saki ko komawa matarsa, sai a tsare shi har sai ya yi daya daga ciki.

5.   Wanda ya sha giya da Ramalan sai a yi masa haddi da tsarin kwana daya da kuma Karin wani Ta’aziri.

6.   Wanda ya rike wani mutum wani kuma ya zo ya kashe shi, to za a tsare shi rai da rai.

7.   Wanda ya yi kisan ganganci da aka kyale shi aka yafe masa, to ana tsare shi wata mudda.

8.   Mai shaidar zur.

9.   Sarkin kasuwa da ya yi ha’inci.

10.    Wanda ya gaya wa mai laifi hujjar da zai cuci musulmi da ita.

11.    Wanda ya kashe bawansa ana tsare shi shekara bayan diyya da bulala dari.

12.    Wanda ya yi sata ta uku. Da makantansu.

 

NAU’IN FURZIN DA KASHE-KASHENSA

Yana da kyau ya zama an raba Gidan Sarka kamar haka; Gidan Sarka na maza da na mata ko na yara da tsofaffi da na manya, kamar yadda yana da kyau a raba masu laifi mummuna ko miyagun tunani da akidu da wasunsu, wannan duk domin gudun fasadi da kuma lalata wasunsu maimakon kawo gyara a gare su, kamar yadda hakkin kowane ne daga cikinsu a ba shi dakinsa daban.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next