Boyayyar Taska



Mahangar Ahlul Baiti (A.S) game da ma'asumai da Allah (S.W.T) ya sanya su hujja kan al’umma bayan Manzon rahama su goma sha biyu ne, idan ka hada da Ma'asumiya Sayyida Zahara (A.S) Ma'asumai sun zama goma sha hudu kenan, wato Manzon Allah (S.A.W) da Fadima (A.S) da halifofinsa goma sha biyu (A.S) da ya yi wasiyya da bin su.

Takaitaccen Tarihin Manzo Da Ahlin Gidansa

Manzo Muhammad Dan Abdullahi Al-Habib

Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Abdullahi dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan Kusayyi dan Kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga Annabi Ibrahim (A.S).

Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu ‘yar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan Kilabi.

Alkunyarsa: Abul Kasim, Abu Ibrahim.

Lakabinsa: Almusdafa yana da sunaye da suka zo a cikin Kur’ani mai girma kamar, Khataman nabiyyin, da Al’ummi da Almuzzammil da Almuddassir da Annazir da Almubin da Alkarim da Annur da Anni’ima da Arrahma da Al’abdu da Arra’uf da Arrahim da Asshahid da Almubasshir da Annazir da Ad’da’i da sauransu.

Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash’hurin zance gun Ahlul Baiti (A.S), an ce, 12 ga watan da aka ambata.

Wurin haihuwarsa: Makka.

Aikoshi: An aiko shi a Makka 27 Rajab yana dan shekara arba’in.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next