Boyayyar Taska



2.      Kuma shin zai yiwu ta kira mutane zuwa ga mijinta da neman yi masa bai’a a matsayin halifan da babanta ya bari kuma ya yi wasiyya da shi ba tare da wani dalili ba?

3.      Sa’annan su waye wadannan halifofi goma sha biyu da Manzo (S.A.W) ya yi wasiyya da su bayansa kamar yadda ya zo a littattafan dukkan musulmi shi’arsu da sunnarsu, kamar Littafin Sahih Muslim?.

4.      Kuma shin hankali zai iya bayar da adadain sarakunan Umayyawa ko na Abbasawa masu yawa haka a matsayin su goma sha biyun? Ko kuma halifofi uku na farko?. mai karatu amsa wannan tambayoyi da gano jawabinsu sahihi shi ne zai iya sanyawa ka gano wannan taskar da aka sanya rasid din shiga Aljanna a cikinta.

 Akwai ra’ayoyin masu nazari mabanbanta a game da su waye wadannan goma sha biyun amma muhimmin binciken da zan fi bayar da karfi a kai a nan shi ne, su waye wadannan Ahlul Baiti da Manzo (S.A.W) ya bar wa al’umma tare da Kur’ani mai girma da ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske shi a tafki kamar yadda suka zo a ruwayoyi.

Su Waye Ahlul Baiti Halifofin Manzo (S.A.W)

Ya zo cewa Manzo (S.A.W) ya bar Kur’ani da Ahlul Bait (A.S) ga al’ummarsa, abin tambaya shi ne su waye wadannan Ahlul Bait kamar yadda ya zo a littattafan hadisai?, Manzo (S.A.W) da kansa ya bayyana wa al’umma su waye Ahlin Gidansa tsarkaka kuma masu daraja wajan Allah kuma halifofinsa kamar haka;

Yayin da Ayar nan ta Suratul Ahzab: 33 ta sauka, wato; “Hakika kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gare ku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa”[11]. Sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husaini (A.S) ya lullube su da wani bargo da aka yi wa zane da bakin gashin rakumi. Wannan Hadisi[12] ya zo a littafin Muslim, da Buhari, da Mustadrik Alassahihaini, da Tirmizi da Abu Dawud da Tafsirin Bagawi, da Ibn Kasir, da gomomin Tafsirai da Littattafan hadisai, kamar yadda wannan hadisin ya maimaitu a lokacin mubahala da kiristocin Yaman da sauran wurare da dama.

Akwai wata mahanga da take ganin cewa Ahlul Baiti (A.S) su ne Alayan Ali, da Ja’afar, da Akil, da Abbas, wannan shi ne nazarin Zaid Dan Arkam. Amma kuma duk mahangan sun hadu a kan kore matan Annabi (R.A) daga kasantuwa cikin Ahlul Baiti. Game da mahangar Zaid kuwa muna iya cewa; idan aka ce ga maganar Manzo (S.A.W) ka sani cewa ba wata magana da take da kima bayanta.

Kamar yadda ruwayoyin sun yi nuni da cewa Ummu Salama (R.A) ta so ta shiga cikinsu amma Manzo (S.A.W) da kansa ya nuna mata ba ta cikin Ahlul Bait (A.S). Akwai kuma wasu hadisai da suka yi nuni da cewa; Ahlul Bait (A.S) su biyar ne da kuma tara daga ‘ya’yan Husain (A.S). Wato halifofinsa guda goma sha biyu da kuma Fadima (A.S) wanda na farkon su shi ne Ali (A.S) na karshensu shi ne Mahadi (A.S)[13].

Ya zo a Tafsirin Ibn Kasir a tafsirin Aya ta 55 ta Surar Ma’ida cewa[14]: Daga Maimun Dan Mahran daga Ibn Abbas, a fadin Allah mai grima da buwaya:  “Kawai majibancin lamarinku (Jagoranku) Shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadanda suke tsayar da Salla suke bayar da Zakka alhalin suna masu ruku’u”. Yana mai cewa: Ta sauka ne game da Muminai kuma Ali Dan Abu Talib (A.S) Shi ne na farkonsu. Wato tana mai nuni da cewa na farkon wadanda za a mika wa wilaya da Shugabanci bayan Allah da Manzonsa shi ne Ali (A.S) Sa’annan masu biyo wa bayansa na daga wasiyyai, kamar yadda zamu ga ta sauka ne a lokacin da ya yi sadakar zobensa alhalin yana cikin ruku’i. Wasu littattafan suna cewa; ta sauka game da muminai Ali (A.S) ne na farkonsu, Mahadi (A.S) na karshensu[15].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next