Boyayyar Taska



Fifita Wasu Mutane A Kan Manzo (S.A.W)

Sannan mafi yawansu a aikace suka ci gaba da ganin sarakunan Kuraishawa da na Usmaniyawa a matsayin rukunai ne daga rukunan Addinin musulunci da Allah (S.W.T) ya saukar wa manzonsa (S.A.W) da su tare da sauran rukunonin Addini, kuma duk wani abu da yake kishiyantar halifofi yake sukansu to a tunanin mafi yawansu shi wannan ya kafirce wa Allah da Manzonsa. Ta haka ne halifofin Kuraish da na Usmaniyya suka zama wani yanki daga yankin musulunci a wajansu, kai shi ne ma yanki mafi girma a zukatansu, har ba ka isa ka samu wanda yake kishin Allah da Manzonsa ba kamar yadda yake kishin wadannan halifofin Umayyawa da Abbasawa.

Har ma akwai wani malami mai fassara a kasashenmu da aka taba cin zarafin Manzon Allah, da mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) suka tashi a kan haka sai ire-irensa suka ce: “Ai kotu ake kaiwa”. Amma wani abin mamaki shi ne sai ga irinsu suna yin karya a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) wai suna zagin Sahabbai! Har ya ce: Suna zagin Sayyidina Umar! Ya kuma fashe da kuka yana mai cewa: Mutane suna gani ba su yi komai ba! Abin mamaki da tambaya a nan shi ne, bai taba jin zagin wani sahabi daga garesu ba, kuma bai taba ganin wanda ya ji zagin ba, amma sai ga shi yana kuka a Gidan Radio /Talabijin yana kuma neman a dauki mataki a kai.

Amma sai ga shi yana da tabbacin an ci mutuncin Annabi, kuma ba wanda ya tashi ya nuna fushinsa a wancan lokaci sai mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) amma yake sukan abin da suka yi wai me ya sa ba su je kotu ba, kuma ba a ga ya nuna koda bakin ciki ba da cin mutuncin da aka yi wa Annabi (S.A.W), balle ma ya yi kukan cin mutuncin, wannan duk yana daga mummunar tarbiyyar da guggubin mulkin Sarakunan Daulolin Umayyawa da Abbasawa da Turkawa suka bari ta hanyar nuna darajarsu da rashin ko in kula da daukaka darajar Fiyayyen halittu, Ma’aiki (S.A.W).

Tambaya a nan shi ne a lokacin da aka ci zarafin Manzon Allah da kalmomin da idan aka gaya wa duk wani wanda mutum yake so irinsu sai ya dauki mataki me ya sa ba mu ga irinsa ya yi kukan ba?, abin mamaki ba ma ya yi kuka ba, shi yana ma ganin laifin wadanda suka ce ba su yarda ba ne, yana ma ganin laifinsu ne alhali a kan kare Manzon (S.A.W) kuma da kona jaridar da ta ci mutuncinsa wasunsu ma sun rasa rayukansu, wasu kuma sun yi gidan kaso ko sun rasa wasu gabobi nasu.

 Haka nan irin wadannan mutane suke kulla gaba da mabiya Ahlul Bait (A.S) a kwakwalensu ba tare da sun kafa wani dalili kwakkwara ba a kan haka, ina ganin wannan suka da kagen karya da aka fara shi a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) tun lokacin sarakunan Umayyawa da Abbasawa ya kuma yi tsanani a lokcin Usmaniyawan Turkawa yana da kyau mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) su dauki mataki a kansa koda kuwa ta hanyar kotuna da rubuce-rubuce da kuma gidajen watsa labarai ne, domin su kunyata irin wadannan mutane da suka zamanto ragowa ne su na kage da farfagandar kakanninsu na lokacin da ya shude a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S).

Aikin Mutum Ba Ya Iya Nuna Mazhabarsa

Yana da kyau mu sani cewa mazhabar Ahlul Baiti (A.S) daban aikin mabiya mazhabar daban, yana yiwuwa ya yi daidai ko ya saba da koyarwar mazhabar don haka ba a duba aikin mutum a ce haka mazhabarsa take, domin musulunci daban aikin musulmi daban, idan muka gane haka warware abubuwa da dama zasu yi sauki.

Wata rana wani daga masu sukan mabiya Ahlul Bait (A.S) ya ce: Daga Akidar mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) shi ne shan taba. Sai na ce da shi: Da zaka ce: Daga Akidar Malikawa ko Hanifawa akwai shan taba da za a sha mamakin jahilcinka, domin a lokacin Maliku babu taba ballantana Imam Ali (A.S) da yake shi ne Imamin mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S).

Na farko da sai da ya yi shahada da shekara hamsin da wani abu sannan aka haifi Maliku, na biyu kuma wannan furu’a ne ba Akida ba. Abin da yake yi wa mutane da yawa wahalar ganewa sakamakon jahilci da ya yi kanta cikin al’umma, na kara masa da cewa: Don haka ne nake gaya maka ina kare mazhabin Ahlul Baiti (A.S) ne ba ina kare mabiyansu ba domin zai iya yiwuwa aikin nasu ya saba da mazhabin. Na ce da shi: Da wani kirista zai ji ka yi karya sai ya ce da kai: Lallai musulunci ba shi da kyau. Sai ka tambaye shi; saboda me?. Sai ya ce: Saboda ka yi karya kuma wannan yana nuna karya tana daga Akidun musulunci, ya ya zaka ba shi amsa?. Sai ya ce: Amsar da na bayar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 next